….Nauyin Aikin Da Ke Najeriya Da Ban tsoro, Inji Femi
Daga Imrana Andullahi
Shugaba Bola Tinubu ya bi sahun sauran Musulman Najeriya da sauran duniya baki daya domin gudanar da Sallar Eid-el-Kabir a filin Sallar na Barikin Dodan da ke Legas.
Shugaban ya samu rakiyar Nuhu Ribadu, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro; Femi Gbajabiamila, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa; Babatunde Fashola, tsohon gwamnan jihar Legas da sauran manyan jami’an Gwamnati.
A cikin hudubarsa, babban limamin Legas, Sheikh Suleiman Abu-Nolah, ya ce bikin na inganta al’adun sadaukarwa, hadin kai da kuma hakuri da juna a tsakanin musulmi masu imani kuma mabiya addinin Musulunci.
“Addini bai yarda da aikata son kai, rashin hakuri ko bangaranci ba.”
Ya kamata mu yi amfani da wannan damar wajen yin tunani a kan kalubale daban-daban da kasar nan ke fuskanta, mu yi amfani da ita wajen gyara duk wani kalubalen da muke fuskanta ta hanyar yin addu’a ga Allah Madaukakin Sarki,” inji shi.
Babban limamin ya yi addu’ar Allah ya kara wa Nijeriya zaman lafiya, ci gaba da kwanciyar hankali, ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi koyi da darajojin Annabi Ibrahim.
Femi Hamzat, mataimakin gwamnan jihar Legas, ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi wa kasa addu’a.
Dole ne mu sadaukar wa kasa domin yin addu’a da soyayya wani bangare ne na aikinmu na ‘yan kasa domin shi ne zai kara daukaka al’umma,” inji shi.
Shi kuma Femi Gbajabiamila, a nasa jawabin,cewa ya yi shugaban kasar zai ci gaba da baiwa ‘yan Najeriya fata ta hanyar ci gaba da aiwatar da manufofin da suka dace da jama’a.
Ya ce shugaban kasar zai bukaci addu’ar ‘yan Najeriya don ci gaba da tsare-tsare daban-daban na mayar da kasar nan mafarkin iyayenmu da Kakannin mu suka gabata.
Yayin da shugaban kasa ya dawo Abuja, zai bukaci addu’o’in ku, kuma yayin da yake tafiya duk lungu da sako na Nijeriya, shi ma zai bukaci addu’o’in ku.
“Nauyin aikin yana da ban tsoro amma tare da addu’a da goyon bayan dukkan ‘yan Najeriya, shugaban kasa zai yi nasara a kansu,” in ji shi.