Daga Imrana Abdullahi
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai yi jawabi ga al’ummar kasar a ranar Litinin, 31 ga Yuli, 2023 da karfe 7 na yamma.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Dele Alake
Mai bawa shugaban kasa shawara na musamman (Ayyuka na musamman, Sadarwa & Dabaru) da aka fitar domin sanar da jama’ar kasa.
An umurci gidajen Talabijin da gidajen rediyo da sauran kafafen yada labarai na zamani da su rika cudanya da ayyukan sadarwar Hukumar Talabijin ta Najeriya da Rediyon Najeriya domin yada shirye-shiryen jawabin da shugaban kasar zai yi da Yammacin yau.