Home / Big News / Sojoji Sun Yi Nasarar Halaka Dan Ta’adda Gana

Sojoji Sun Yi Nasarar Halaka Dan Ta’adda Gana

Sojoji Sun Yi Nasarar Halaka Dan Ta’adda Gana

Imrana Abdullahi

Jami’an rundunar sojan tarayyar Nijeriya da ke aiki da rundunar AYEM APKATUMA sun samu nasarar halaka fitaccen dan ta’addan nan da ke jagorantar miyagu a yankin Banuwai Banuwai suna Tarwase da ake wa lakabi da Gana.

Sojojin sun bayyana hakan ne a lokacin da suka kira taron manema labarai a ranar Talata da Dare a karamar hukumar Doma da ke Jihar Nasarawa, a hedikwatar rundunar tsaro ta Kwamand inda ake nunawa manema gawar Gana, kwamandan, Mejo Janar Moundhey Gadzama Ali ya ce “Na gayyato ku ne a wannan yammaci domin ku shaida wani labari da dumi duminsa da jami’an soja masu aiki a karkashin rundunar AYEM APKATUMA III.

” Da misalin karfe 12 na ranar yau muka samu sahihan bayanai a game da irin yadda Dan Ta’adda Terwase Akwaza Agbadu da aka fi Sani da Gana a kan titin Gbese – Gboko da ke kan titin Makurdi.

“Jami’an sojan na AYEM APKATUMA III nan da nan suka yi shiri sai kan hanyar da tawagar dan ta’addan zai wuce suk kuma kafa shinge da misalin karfe daya, saboda akwai sadarwa tsakanin soja da tawagar dan Ta’adda Gana.

“Da isowarsu sai harbi nan take aka tabbatar da cewa lallai ya halaka. A lokacin gudanar da bincike, an gano wadannan tarin makamai, bindigar Qty 5 AK 47,Qty 1 FN rifle, karamar bindigar fistol, babbar bindigar  Qty3 pump action, bindiga kirar gargajiya ta mashingan, bindigogi 10 kirar  Dane, bindigar fistol 19, bindiga 35 kirar gida ta ribal ba da bindiga kirar gida ta Mortars guda 2.

Sai kuma sauran sun hada da albarusai, kamar yadda aka bayyana guda 766 na musamman masu milimita 7.62 da milimita 27.9 masu suffar zagaye a jikinsu da wadansu manyan alabarusai bindigogi 26

Ya ce da mashin 1 sai wani tsafin Daurawa Daurawa wasu asiran kuma 2 da kuma abubuwan fashewa guda 2 na gargajiya duk aka samesu a wurinsu

Ya kara da cewa mutane 40 saga cikin mutanensa duk sun shiga hannu a lokacin wannan artabun za kuma a mikasu a hannun hukumar da ya dace domin ayi masu shari’a.

About andiya

Check Also

NASCON grows turnover by 37%, assures Shareholders of Continuous Growth, Value Creation

NASCON Allied Industries Plc has assured its shareholders of continuous growth and value creation in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.