Home / Labarai / Suwaye Ke Kokarin Shirya Zanga – Zanga A Najeriya – Shetima Yarima

Suwaye Ke Kokarin Shirya Zanga – Zanga A Najeriya – Shetima Yarima

 

An yi kira ga daukacin al’ummar Najeriya musamman ma na yankin Arewacin da su natsu domin sanin wadanda ke kokarin shirya Zanga- Zangar da wasu ke ta kururuwar za a yi a Najeriya.
Shugaban kungiyar tuntuba ta matasan Arewa Kwamared Shetima Yarima ne ya yi wannan kiran, inda ya ce hakika duk da ana cikin matsalar tsadar kayan abinci da na sauran abubuwan masarufi, amma dai ya dace a san su waye ke kokarin shirya Zanga zangar da ake ta yin kururuwa a kafafen Sada zumunta ba tare da an san wadanda ke kokarin shirya ta ba don haka lallai mutane su shiga taitayinsu.
“Musamman dai mutanen arewacin Najeriya da ke fama da kalubale iri iri hakika akwai wadannan matsalolin tsadar rayuwa, amma fa duk da haka ya dace kuma ya zama wajibi a san suwaye ke shirya wannan Zanga Zanga domin koma ya faru sakamakon hakan an san wadanda sune keda alhakin yin hakan ba wai kawai a dandalin Sada zumunta na yanar Gizo- Gizo ba da babu wanda ya san masu shirya hakan”.
“Saboda mu a arewacin Najeriya fa akwai kalubale da yawa don haka mu a iya sanin da muka yi wadansu mutane za su iya yin amfani da wannan lamari su rika faffasa dukiyoyi da gidajen wadansu mutane wanda kuma hakan ba dai- dai ba ne a tsari na kasa, don haka mu a matsayin mu na shugabannin kungiyar tuntuba ta Arewa muke fadakarwa domin kada a samu matsala a kan wadda ake da ita a yankin arewacin kasa”.
Babban Burin mu shi ne Najeriya ta ci gaba da zama hamshakiyar kass a duk fadin duniya baki daya.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.