Ta Yi Barazanar Sake Yi Wa Mijinta kaciya
andiya
September 7, 2023
Labarai, News
193 Views
A kokarin kare lafiya da kuma ceton ransa Wani mutum mai suna Malam Ali da ke zaune a birnin Kano ya garzaya Kotun Addinin Musulunci da ka Rijiya Lemo tare shaidawa kotun cewa matarsa ta yi masa barazanar za ta sake yi mashi kaciya.
Akan haka ya roki kotu da ta shiga sakani domin hana matar sake yi mashi kaciya, musamman ganin ta sayo wuka mai kaifin gaske tare da boye wukar a wani wuri cikin gidan da suke zaune.
Ya ce wannan barazana tana ba shi tsoro sosai ta yadda ba ya samun kwanciyar hankali a duk lokacin da ya ke gidanta.
Bayan sauraren karar da Mal Ali ya gabatar, alkalin kotun Malam Sunusi Danbaba Daurawa ya dage sauraron karar sai ranar 4 ga Okutoban 2023 domin ci gaba da shari’a.
A lokacin da manema labarai suka nemi karin haske daga bakin Mal Ali akan wannan al’amari bayan zaman kotu, ya ce ya duba dakin matar tashi, ya ga wukar da ta sayo ta boye, ya kuma dauke wukar daga inda ta boye ta, amma har yanzu hankalinsa bai kwanta ba
Ya ce shi dai bai san abin da ya faru ba, amma ta ce sai ta sake yi mani kaciya. Ina zaune lafiya da ita amma wannan ita ce matsalar da ni ke fama da ita, kuma shi ne dalilin zuwa na gaban alkali domin a hana ta aikata wannan aiki.
Amma a lokacin da manema labarai suka nemi jin ta bakinta sai matar ta ki yin magana.