Gwamna Dauda Lawal ya ƙaddamar da sabon Tsarin Ci Gaban Jihar Zamfara na 2025 zuwa 2034, wani tsari mai dogon zango da aka gina bisa bincike, bayanai, da tattaunawa da ƙwararru domin sake fasalin jihar a shekaru goma masu zuwa. An gabatar da shirin ne a sakateriyar JB Yakubu …
Read More »Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara na Naira Biliyan 140
Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa tana gudanar da manyan ayyukan raya ƙasa da darajarsu ta kai kusan Naira Biliyan 140 a faɗin ƙananan hukumomi 14 na jihar, a wani shiri da aka bayyana a matsayin sabon babi na farfaɗowa da ci gaban Zamfara. A cikin wata sanarwa da ya …
Read More »An Yi Wa Yara Sama Da Miliyan Biyu Allurar Rigakafin Mashaƙo Da Sankarau A Zamfara
A Zamfara, hukumomin kula da yaƙi da cutar shan-inna sun bayyana cewa an yi wa yara fiye da miliyan biyu rigakafin cututtukan mashaƙo da sankaran yara a faɗin jihar, yayin da sama da miliyan 1.8 na yara ‘yan ƙasa da watanni 59 suka karbi rigakafin cutar shan-inna. Jami’in kula …
Read More »Muna Sauya Zamfara Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na gina jihar da ke tafiya bisa tsarin zamani mai dogaro da fasahar zamani. A ranar Talata, gwamnan ya buɗe shirin horas da kwamfuta ga kwamishinoni da manyan masu ba da shawara na musamman, a fadar gwamnati da ke Gusau. …
Read More »Gwamna Lawal Ya Jagoranci Ƙaddamar Da Kwamitocin PDP Gabanin Babban Taron Jam’iyyar
Gwamna Lawal Ya Jagoranci Ƙaddamar Da Kwamitocin PDP Gabanin Babban Taron Jam’iyya Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da kwamitocin tantancewa da na ayyuka na musamman na jam’iyyar PDP a ranar Juma’a, a shirye-shiryen gudanar da babban taron gangamin jam’iyyar mai zuwa. An tsara babban taron zaben shugabannin jam’iyyar …
Read More »Gwamnatin Zamfara Ta Kammala Zagaye Na Goma Na Aikin Jinya Kyauta, An Kula Da Marasa Lafiya 3,447
Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa ta kammala zagaye na goma na shirinta na musamman na aikin jinya kyauta, inda aka kula da marasa lafiya 3,447 daga sassa daban-daban na jihar. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya ce shirin wanda …
Read More »Dole Arewa Ta Yi Magana Da Murya Ɗaya Kan Tsaro Da Tattalin Arziki, In ji Gwamnan Zamfara
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya buƙaci jihohin Arewa 19 da su tsaya ƙyam su jajirce su yi magana da murya ɗaya kan harkokin tsaro da tattalin arziki. Gwamnan ya jagoranci taron ranar farko ta bangaren Zuba Jari da Bunƙasa Masana’antu ta Arewacin Nijeriya a ranar Litinin a otel ɗin …
Read More »Gwamnonin PDP Za Su Yi Taro A Gusau Jihar Zamfara
Daga Imrana Abdullahi Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal zai karbi baƙuncin ɗaukacin gwamnonin jihohin da jam’iyyar PDP ke mulki, inda za su tattauna muhimman batutuwan da suka shafi jam’iyyar da ƙasa baki ɗaya a Gusau, babban birnin jjhar. Yau Juma’a ne ake sa ran isar gwamnonin a Gusau don shirin …
Read More »Ba Za Mu Taba Yin Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba, Inji Gwamnan Zamfara
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya sake nanata matsayar sa kan sulhu da ‘yan ta’addar da ke kashe mutanen Zamfara ba dare ba rana, inda ya ce ba zai taba yin sulhu da su ba. Gwamnan ya faɗa wa mutanen Zamfara cewa gwamnatinsa ba za ta taba yin sulhu …
Read More »Gwamna Lawal Ya Jaddada Aniyar Inganta Kiwon Lafiya A Jihar Zamfara, Ya Ƙaddamar Da Babban Asibitin Gusau Da Aka Gyara
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada ƙudirinsa na sake farfaɗo da tsarin kiwon lafiya a Jihar Zamfara, tare da cika alƙawarin gwamnatinsa na samar da nagartacce kuma ingantaccen kiwon lafiya ga al’umma. Gwamnan ya ƙaddamar da Babban Asibitin Gusau da aka gyara ciki-da-bai a ranar Juma’a. A wata …
Read More »
THESHIELD Garkuwa