Home / Labarai / Talakawan Jihar Zamfara Na Bukatar Samun Tsaro – Bashir Nafaru

Talakawan Jihar Zamfara Na Bukatar Samun Tsaro – Bashir Nafaru

Daga Imrana Abdullahi

Wani jagoran al’ummar Jihar Zamfara kuma fitaccen dan siyasa daga karamar hukumar Talatar Mafara, Alhaji Bashir Nafaru ya kara jaddada kira ga Gwamnatin Jihar Zamfara da ta kara himma wajen samar da ingantaccen tsaro ga al’ummar Jihar musamman ma Talakawa.

Bashir Nafaru ya yi wannan kiran ne a wata tattaunawa da wakilin mu.

Nafaru , ya ci gaba da cewa duk da Gwamnatin jihar na kokari wajen harkar tsaro, amma akwai bukatar a kara kaimi domin a wadansu wurare lamarin tsaro na neman kazancewa, saboda Talakawa a yanzu ne mutum yanzu ba mutum ba.

“Yanzu sai kaji an gaisa da mutum amma zuwa an Jima sai kawai lanarin an kashe shi, wanda hakan na Jefa dimbin talakawan Jihar Zamfara cikin wani hali na daban”.

Nafaru, ya kara da cewa ” a yau ranar 20 ga watan Disamba, 2023, hakika muna kallon takun sakar Gwamnatin Jihar, a cikin kananan hukumomi Goma sha hudu (14) da muke da su a cikin Jihar Zamfara a karamar hukumar Gusau ne kawai muke ganin ana aiwatar da ayyukan raya kasa saboda haka ne muke kara ankarar da Gwamnati a kan wannan tafiyar hawainiyar domin kada a ware wadansu kananan hukumomi amma ana aiwatar da aiki a wasu hakan  akwai gyara kwarai . Mu bamu ta ba ganin inda ake Dimokuradiyya ayi aiki a wani wuri amma kuma a bar wadansu ba, saboda haka ne muke yin kira ga Gwamnati da ta duba matsalolin sauran kananan hukumomi Goma sha uku a san abin da za a yi masu”.

Sai dai Bashir Nafaru ya ce suna godiya ga Allah madaukakin sarki da duk da matsalar tsaron da ake fama da shi Gwamnatin Jihar Zamfara na yin iyakar bakin kokarinta. Don haka muke rokon Gwamnati domin Allah don Allah don Allah a taimakawa talakawan da suke cikin daji yan uwan mu domin babu abin da ake bukata sai a samu ingantaccen tsaro saboda rayuwar mu Talakawa na cikin wani hali na rashin tabbas yanzu za a gaisa da mutum idan an Jima sai ace an kashe mutum kawai”.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.