Home / Labarai / Tinubu Ya Dakatar Da Shugaban Hukumar EFCC

Tinubu Ya Dakatar Da Shugaban Hukumar EFCC

Shugaban tarayyar Najeriya  Bola Tinubu ya dakatar da Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Willie Bassey ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fita

Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC.

Daraktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya Willie Bassey ya sanar da hakan.

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya amince da dakatar da Mista AbdulRasheed Bawa, CON daga ofishin Mista AbdulRasheed Bawa, CON, a matsayinsa na Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) don ba da damar gudanar da bincike mai kyau a kan yadda ya aikata yayin da yake kan mulki.

“Wannan ya biyo bayan zarge-zargen cin zarafi da aka yi masa.  An umurci Mista Bawa da ya gaggauta mika al’amuran ofishinsa ga Daraktan Ayyuka a Hukumar, wanda zai kula da harkokin ofishin Shugaban Hukumar har sai an kammala bincike.

About andiya

Check Also

Backward Integration: Dangote Targets 700,000MT of Refined Sugar in Four years

    …As Q1 revenue rise by 20.1% to N122.7bn   Dangote Sugar Refinery Plc …

Leave a Reply

Your email address will not be published.