Home / Labarai / Tsadar Rayuwa: Kungiyar Kwadago Za Ta Tsunduma Yajin Aiki

Tsadar Rayuwa: Kungiyar Kwadago Za Ta Tsunduma Yajin Aiki

Daga Imrana Abdullahi
Sakamakon irin tsananin rayuwa da ta haifar da cakudewar al’amura a birane da karkarar daukacin tarayyar Najeriya yasa kungiyar kwadagon kasar ta fitar da wata sanarwar tsunduma yajin aikin sai illa masha Allahu wato kamar dai yadda masu iya magana ke cewa sai Baba ta gani.
Kamar dai yadda wakilin mu ya ji ana fadi a kusan dukkan wuraren taruwar jama’a da Kasuwanni da wuraren cin abincin jama’a kowa na kokawa da irin matsanancin karuwar farashin komai da mutum dan Adam zai yi amfani da shi duk da cewa kusan dukkan al’ummar Najeriya na yin rayuwa ne irin ta hannu baka hannu kwarya.
Kuma ko a bangaren Gwannati ma a halin da ake ciki akwai wadansu Jihohin da ke da matsalar yaya ma za su yi domin biyan Albashin ma’aikatan da ke aiki a Jihar da kuma Kananan hukumomi saboda kamar dai yadda lamarin yake ko a matakin kananan hukumomin ma wasu da dama idan za a barsu hakika ba za su iya biyan albashin ma’aikatan su ba.
Wadannan da ma wadansu dalilai masu taron yawa ya Sanya babbar kungiyar Kwadago ta kasa ta yanke shawarar tsunduma ciki yajin aiki
Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta bai wa gwamnatin Bola Tinubu wa’adin kwana bakwai ta janye duk tsare-tsaren da ta kira ”masu jefa jama’a cikin wahala” ciki har da ƙarin farashin man fetur.
A cikin wata sanarwar bayan taro da ƙungiyar ta fitar, NLC ta yi barazanar fara yajin aikin sai-baba-ta-gani daga ranar Laraba, 2 ga watan Agustan 2023, idan gwamnatin tarayya ta gaza ɗaukar matakin da ya kamata.
Sanarwar mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero da sakatarenta Emmanuel Ugboaja ta ambato NLC na cewa gwamnatin tarayyar ta nuna halin ko-in-kula kan halin da ‘yan ƙasar ke ciki, kuma ta ce gwamnatin ta kaddamar da yaƙi ne a kan ma’aikata da talakawa.
Ƙungiyar ƙwadagon ta ce tun daga lokacin da shugaba Tinubu ya sanar da janye tallafin mai a jawabinsa na rantsuwar kama aiki, ”hankalin ‘yan Najeriya bai kwanta ba”.
Ita dai gwamnatin Najeriya ta ce cire tallafin man fetur ɗin ya zama wajibi a halin da ƙasar take ciki, matuƙar tana son samun kuɗaɗen gudanar da muhimman ayyuka.

About andiya

Check Also

Northern govs meet in Kaduna, design regional economy, human capacity devt

    The chairman, Northern States Governors’ Forum (NSGF), Muhammadu Inuwa Yahaya, has called for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.