Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Olufemi Oluyede, ya yaba da irin gagarumin goyon bayan da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ke bai wa rundunar Operation Fansan Yamma, yana mai cewa irin wannan tallafi ba kasafai ake ganin irinsa ba.
Janar Oluyede ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyarar aiki da ya kai Jihar Zamfara, inda ya gana da gwamnan tare da duba hedikwatar rundunar Operation Fansan Yamma da ke Gusau.
A lokacin ziyarar girmamawa da ya kai Gidan Gwamnatin Jihar Zamfara, Babban Hafsan Tsaron ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin gwamnatin jiha da rundunar sojoji wajen magance matsalolin tsaro da suka addabi yankin.
Ya ce, ya zo jihar ne domin nuna godiya ga gwamnan bisa irin rawar da yake takawa wajen tallafa wa rundunar, yana mai ƙarawa da cewa haɗin kai tsakanin gwamnati da al’umma na da matuƙar muhimmanci wajen shawo kan ƙalubalen tsaro.
Janar Oluyede ya kuma yaba wa al’ummar jihar bisa yadda suke karbar jami’an tsaro hannu bibbiyu, yana mai jaddada cewa Nijeriya ƙasa ɗaya ce da ke buƙatar haɗin kan kowa domin fuskantar barazanar tsaro.
Ya ƙara da cewa, ya ziyarci hedikwatar rundunar Operation Fansan Yamma, inda ya gana da jami’an tsaro, ya saurari ƙalubalen da suke fuskanta, tare da warware wasu daga cikinsu, yayin da sauran aka ɗauki matakan da suka dace domin magance su nan gaba.
A nasa bangaren, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa magance matsalar ‘yan bindiga a Zamfara na nufin an rage kusan kashi 75 cikin 100 na matsalar a duk faɗin Nijeriya.
Ya ce, wajibi ne shugabanni su ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a, yana mai jaddada cewa babu wani ƙarfi da ya wuce na rundunar sojojin Nijeriya.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin sa na ci gaba da bayar da cikakken goyon baya ga jami’an tsaro, yana mai tunatar da cewa a kwanan nan Ministan Tsaro ya ƙaddamar da sabbin motocin aiki na zamani da gwamnatin jihar ta samar domin taimaka wa rundunar.
Ya kuma jaddada cewa duk wani ci gaba ba shi da amfani idan babu tsaro, don haka ne gwamnatin jihar ke bai wa bangaren tsaro fifiko a cikin manufofinta.
Gwamna Lawal ya gode wa Shugaban Ƙasa bisa tallafin da yake bai wa jihar, tare da jaddada buƙatar ƙarin goyon baya domin cimma nasarar yaƙi da matsalar tsaro.
A ƙarshe, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki kafaɗa da kafɗa da rundunar sojoji da sauran hukumomin tsaro domin kawo ƙarshen matsalar ’yan bindiga a jihar.
THESHIELD Garkuwa