Related Articles
Daga Imrana Andullahi Kaduna
Bayanan da muke samu daga cikin garin Kaduna na cewa tsohon shugaban kamfanin buga takardun New Nigeria da Gaskiya Ta Fi Kwabo Malam Tukur Othman ya rasu a safiyar yau Juma’a nayan fama da rashin lafiya, ya kuma rasu ne a asibitin Garkuwa da ke cikin garin Kaduna.
Bayanin sanarwarbrasuwar tasa na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun mawallafin jaridar Desert Herald Tukur Mamu, da aka Sani mai tattaunawa domin shiga tsakanin wadanda aka kama da wadanda suka kama kuma suka yi Garkuwa da fasinjojin Jirgin kasa da aka kama a kan hanyarsu daga Abuja zuwa Kaduna.
Marigayi malam Tukur Othman ya rasu ya bar mata biyu da yaya Goma sha Shida 16, kamar dai yadda sanarwa daga iyalansa ta bayyana.
Kuma kamar yadda sanarwar da ke dauke da sa hannun mawallafin jaridar Desert Herald Malam Tukur Mamu, (Dan – iyan Fika), ya fitar ta ci gaba da bayanin cewa “Hakika an yi rashin mutumin da ya jajirce wajen yi wa kasa da al’ummarta hidima, don haka muna mika ta’aziyyar mu ga yan Najeriya da daukacin kamfanonin wallafa jaridu baki daya, muna kuma yi wa iyalansa ta’aziyya da magoya a madadin kamfanin sadarwa na FUZA Communication Services Ltd.
“Kuma za a yi Sallar Jana’izarsa ne a masallacin Mishahu, Unguwar Rimi, Kadaria, da zarar an kammala Sallar juma’a.
Allah ya sa tsawon lokacin da ya dauka ya na rashin lafiya ya zamar masa kaffara, tare da samun shiga Aljannah Firdausi”, inji takardar.