Home / News / APC Ce Za Ta Samu Nasara A Zaben 2023  – Abu Ibrahim

APC Ce Za Ta Samu Nasara A Zaben 2023  – Abu Ibrahim

….Ba Shakka APC Za Ta Lashe Zaben Jihar Katsina
Daga Imrana Abdullahi
Jigo a jam’iyyar APC a tarayyar Najeriya Sanata Abu Ibrahim, ya bayyana cewa jam’iyyar APC ce za ta lashe zaben shekarar 2023 mai zuwa.
Sanata Abu Ibrahim ya bayyana cewa a halin yanzu dukkan wurare ko Jihohin da ake da rashin jituwa tsakanin wadanda suka yi takarar fitar da dan takara a jam’iyyar ana nan an gano wuraren zaku ma ayi abin da ya dace na tattaunawa domin dai – daita wa tsakanin dukkan bangarorin da suke da wata matsala da nufin APC ta ci gaba da samun tabbatarciyar nasara.
Ya bayyana cewa APC ta yi ayyukan da ba a taba tsammanin za a yi su ba, na rubuta littafin a kan irin ayyukan da APC suka yi domin ci gaban rayuwar jama”a.
” dole a zauna a tabbatar an gayawa jama’a irin ayyukan da APC ta yi a Najeriya ta yadda kowa zai san me aka yi, duk da ba kudi amma an yi wa jama’ar Najeriya aiki. Batun irin fitintunun da suke faruwa na rashin tsaro a Najeriya Bola Tinubu na nan ya na duban yadda zai magance wannan matsalar idan Allah ya bashi nasarar zama shugaban Najeriya, kasancewarsa mutum mai dimbin basira”, inji Abu Ibrahim.
Sanata Abu Ibrahim ya ci gaba da bayanin cewa a matsayinsa na wanda ake yi wa lakabi da shugaban Maja, kasancewarsa na wanda ya lashe zabensa da gagarumin rinjaye da ya lashe mazabu 117 da suke a shiyyar Funtuwa, wanda hakan ya wuce yawan kuri’un da Sanatocin yankunan Daura da Katsina suka samu a lokacin da ya tsaya takarar Sanatan yankin Funtuwa, ” domin na samu yawan kuri’u sama da dubu dari biyar duk ya wuce sauran sanatocin Jihar katsina guda biyu.
“Bola Tinubu ya taimaki Buhari ya ci zabe kowa ya san hakan, kuma mu da muke zama da Bola Tinubu mun san irin basirar da yake da ita a game da dukkan abubuwan da za a yi, Tunubu, mutum ne mai dimbin Basira kwarai da ke da bin diddigin ayyukan da Gwamnatin da yake yi wa jagoranci take aiwatarwa a koda yaushe.
Abu Ibrahim ya kara da cewa ya na yi wa al’ummar Najeriya busharar cewa za su amfana kwarai idan Bola Tunubu ya samu zama shugaban Najeriya domin kullum abin da ke ransa kenan yadda za a samu ci gaban da duniya ke takama da hakan.
Kuma ya dace jama’a su Sani cewa matsalar rashin tsaron nan fa an Gaji lamarin ne daga Gwamnatin PDP da ta gabata, kuma yakamata ayi duba da irin yadda lamarin Boko Haram da sauran yadda lamarin yakasance, ” muna nan muna tattaunawa batun matsalar tsaron nan da kuma ya za a yi da lamarin ya kasance a halin yanzu
Abu Ibrahim ya kara da bayanin cewa APC ta yi aikin da ba a taba tsammani ba, na alkairi da ciyar da kasa gaba kuma ayyukan nan masu dimbin yawa ne ga su nan a duk fadin Najeriya
Saboda haka ” dole ya tashi tsaye a tabbatar an shaidawa jama’a irin abin da APC ta yi wa jama’a,Gwamnatin APC ta ba Jihohi bashi domin a can Jihohin ne jama’a suke wannan ya sa Gwnati ta ba Jihohi makudan kudade domin su tafiyar da johohinsu

About andiya

Check Also

PRESIDENT TINUBU COMMENDS DANGOTE GROUP OVER NEW GANTRY PRICE OF DIESEL

  President Bola Tinubu commends the enterprising feat of Dangote Oil and Gas Limited in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.