Home / Labarai / Tsohon Sarkin Kano Ya Gana Da Tawagar Jaridar Desert Herald

Tsohon Sarkin Kano Ya Gana Da Tawagar Jaridar Desert Herald

 Imrana Abdullahi
Tawagar kamfanin jaridar Desert Herald Herald karkashin jagorancin mawallafinta Malam Tukur Mamu, sun ziyarci tsohon Sarkin Kano Muhammad Sanusi II, a inda yake zaune a lokacin da ya kawo ziyara a garin Kaduna.
A ranar Alhamis ne 27 ga watan Agusta 2020, tawagar gudanarwar kamfanin Jaridar Desert Herald suka ziyarci tsohon Sarkin a masaukinsa da ke Kaduna.
Sarkin Kano na 14 ya karbi tawagar cikin garin ciki da karamci, wannan fitar da tsohon Sarkin Muhammad Sanusi II, a lokacin ziyarar da Malam Tukur Mamu ya kaiwa Muhammad Sanusi II ya mikawa masa Kwafin Jaridar inda ya yi masa addu’ar samun ci gaba da samun taimakon Allah da kariya ga tsohon Sarkin na Kano
Sarki Sanusi ya kuma yabawa jaridar tare da mawallafinta bisa kokarinsu na ci gaba da wallafa jaridar a tsawon lokaci.

About andiya

Check Also

An Bukaci Yayan Jam’iyyar APC Da Su Ci Gaba Da Zama Tsintsiya Madaurinki Daya

….Lukman Ya Daina Surutu, A bari Majalisa ta yi aikin ta Daga Imrana Abdullahi Shugaban …

Leave a Reply

Your email address will not be published.