Home / Labarai / Tsohon Shugaban PDP A Kaduna Ya Rasu

Tsohon Shugaban PDP A Kaduna Ya Rasu

Daga Imrana Abdullahi

Shugaban jam’iyyar PDP na farko a Jihar Kaduna, Ibrahim Yaro Suleiman ya rasu.

Sakataren yada Labarai na Jihar, Abraham Alberah Catoh, a cikin sakon ta’aziyyar da ya fitar a  a ranar Juma’a, ya jajantawa iyalai, yan uwa da daukacin yayan jam’iyyar game da rashin da aka yi.

A cewar sanarwar, Shugaban Jam’iyyar na Jihar Kaduna, Felix Hassan Hyat, da daukacin Kwamitin zartaswa na Jiha, sun mika sakon ta’aziyyarsu ga “yan uwa  shugabanta na farko a Jihar, wanda ya rasu bayan fama da doguwar jinya.”

Sanarwar ta kuma bayyana marigayin tsohon shugaban PDP na farko a  jihar a matsayin hazikin dan siyasa kuma dattijo mai kima, sanarwar ta kuma ce ba za a taba mantawa da irin gudunmawar da Suleiman ya bayar wajen ci gaban jam’iyyar a fadin Jihar baki da kasa baki daya ba.

Jam’iyyar ta kuma mika ta’aziyyarta ga abokansa da masoyansa, tare da addu’ar Allah ya baiwa ‘yan uwa hakurin jure wannan rashin da aka yi.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.