Home / Idon Mikiya / Tsokaci Akan Wasu Kalamai Guda 10 Da Gwamna Wike Yayi Ga Manema Labarai A kan Rikicin JAM’IYYAR PDP.

Tsokaci Akan Wasu Kalamai Guda 10 Da Gwamna Wike Yayi Ga Manema Labarai A kan Rikicin JAM’IYYAR PDP.

Wannan Fassarar Rubutun Rono Omokri ne

 

Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike kuma dan halaliyar jami’yyar mu ta PDP ya yiwa manema labarai jawabi akan halin da ake ciki game da jam’iyyar mu, amma a cikin jawaban sa ya yi wasu kalamai wadanda sun kauce hanya, kuma na yi amana cewa bai yi karya ba. Kawai sai dai ace kwakwalwars na daukar lodi da ya wa sakamakon shugabanci jiha irin Ribas, ba karamin aiki bane dole ya shiga rudu. Toh shi ya sa na yi wannan rubutu domin in yi masa wankin kwakwalwa,

1. Shugaban Jam’iyyar PDP Senator Iyorchia Ayu, babu inda ya yi alkawarin zai sauka daga mukamin sa, idan dan takarar shugabancin kasa daga arewacin Najeriya ya lashe zabe. Sai dai kawai ace abin da ya fada shine zai sauka daga mukamin sa IDAN har Jam’iyyar PDP ta bukace shi da yayi hakan. Kuma tun da har kwamitin zartaswa na Jam’iyyar PDP sun kada kuriar amincewa da shugabancin sa me yasa sai ya yi murabus?

2. Jam’iyyar PDP bata kawo batun karba-karba domin al’ummar arewa ba, illa iyaka ma ace domin kudanci aka kawo batun. Tsohon shugaban Jam’iyyar PDP daga kudanci ya fito, kuma a tsarin Jam’iyyar PDP da kuma yadda aka al’adanta, shugaba na gaba ya kamata ya fito ne daga yankin Arewa.

3. Idan har Wike yana da shaida ta hakika cewa shugaban Jam’iyyar PDP Senator Iyorchia Ayu ba mutum ne mai nagarta ko kuma wanda za a amince masa bane, sai ya gabatar da su a gaban hukumar Yan Sanda ko kuma hukumomin da suka kamata.

4. Zaben fidda gwani na dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar PDP, ba abu ne da aka yi a kudundune ba. A bainar jama’a aka yi kuma kowa ya gani ta kafafen yada labarai na talabijin da rediyo. An bayyana wanda ya yi nasara; da yawa basu samu nasara ba, kuma mutane irin su Saraki, Tambuwal, Mohammed, Hayatudeen, Dele Momodu, Anyim, Fayose, Emmanuel, Momodu da sauransu duk babu wanda yayi korafi a kan abu da ya faru ba daidai bane a zaben.

5. Idan har da gaske ne shugaban Jam’iyyar PDP Sanata Iyorchia Ayu, ya yi wata ganawa ta musamman a boye wadda ba ta dace ba a gidan wani tsohon Janar na soji, sai a gabatar da hujja karara game da zarge-zargen kowa ya gani. Amma ko ma meye, waye ne wanda shugaban Jam’iyyar zai gana da shi? Mambobin APC ko wani wanda muka sani?

6. Babu yadda za a yi Wazirin Adamawa Alh. Atiku ya yiwa Gwamna Wike alkawarin Sanata Ayu zai yi murabus, saboda bashi da wannan hurumi a cikin doka, kuma ba mai mulkin mallaka bane, bai da ikon akan Ayu (wanda kuma dukkan alamu sun tabbatar da Wike ne ya kawo shi).

7. Ta ya ma za a yi mutumin da shi kadai ya kawo shugabanin Jam’iyya har sau biyu a PDP da wasu da dama daga cikin mambobin Majalisar Zartaswa, ya ce wai wannan Jam’iyyar ba ta da adalci?
Kamar ace ne Injiniya ya gina gida sa’ilin kuma ya dawo ya ce gidan bai yi tsari ba, me yake nuni a kan karan kanshi?

8. Wike yace Atiku a zagaye yake da mutanen da ba su da wani tasiri a siyasance, amma me yasa ya janye daga shiga kwamitin yakin neman zabe. Tabbas muna bukatar Wike saboda ya na da mahimmanci a siyasar mu.

9. Jam’iyyar PDP tana da kwamitin zartaswa, kuma zai iya ladabtar da duk wani dan jam’iyya da ya yi ba daidai ba.

10. Duk wani mamba a jam’iyyar PDP yana da tasiri, amma babu wani wanda zai ce idan babu shi zance ya kare.

11. A yanzu abin da ya rage shi ne, kundin tsarin mulki na jamiyar PDP ya fayyace makomar shugaban jam’iyyar Sanata Iyorchia Ayu.

 

 

 

Fassarar Rubutun

*Reno Omokri*

About andiya

Check Also

NASCON grows turnover by 37%, assures Shareholders of Continuous Growth, Value Creation

NASCON Allied Industries Plc has assured its shareholders of continuous growth and value creation in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.