Home / Lafiya / DSS Ta Fara Taron Daraktocin Tsaro Na Jihohi Na 9 A Yobe

DSS Ta Fara Taron Daraktocin Tsaro Na Jihohi Na 9 A Yobe

 

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

 

 

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a ranar Alhamis ta fara taron Daraktocin tsaro na jiha karo na 9 a shiyyar Arewa maso Gabas 2022, zango na uku a Damaturu a wani bangare na kokarinta na duba dabarun inganta zaman lafiya da tsaro a yankin da kuma kare rayuka da Dukiyoyin al’umma.

A lokacin da yake bayani a wajen bude taron, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni wanda mataimakinsa Idi Barde Gubana ya wakilta, ya bayyana godiyarsa ga daukacin hukumomin tsaro na ganin an dawo da zaman lafiya a jihar Yobe.

Ya tuna lokacin da babban birnin jihar Yobe ya zama ba kowa saboda tada zaune tsaye da ‘yan tada kayar bayan suka yi, “idan muka tuna, dukkanmu muna sane da halin da muka shiga, Damaturu a wancan lokacin galibi ba kowa ne kuma muka zama ‘yan gudun hijira, cikin ikon Allah da  kokarin maigirma shugaban kasa kuma babban kwamandan sojojin tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari aka samu zaman lafiya, alhamdulillahi”.

Buni ya yi maraba da mahalarta taron, inda ya bayyana shi a matsayin lokacin da ya dace, yana mai nuni da cewa, taron zai taimaka matuka wajen inganta harkar tsaro a kasar nan daga duk wani nau’i na miyagun laifuka.

Da yake jawabi tun da farko, daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) reshen jihar Yobe Damaturu, Yunusa Abdulkadir ya ce taron na da nufin tattauna batutuwan da suka shafi tsaro yana mai nuni da cewa ayyukan masu ruwa da tsaki kamar su sarakunan gargajiya, malaman addini, malamai, jami’an tsaro, ‘yan uwa mata, Hukumomi, kungiyar ‘yan banga, kafafen yada labarai suma suna da matukar muhimmanci ga hadin kai don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.

Daraktan ya lura cewa wasu daga cikin ‘yan kasar da suka gamu da ajalinsu a lokacin da ake tada kayar kafin nan sun bukaci goyon bayan zamantakewar al’umma don gujewa tabarbarewar doka da oda da ke haifar da wani kalubalen tsaro.

Ya yabawa gwamnatin jihar Yobe da jami’anta bisa goyon baya da hadin kai, wanda a cewarsa ya ba su damar gudanar da ayyukansu.

A nasa bangaren, shugaban taron wanda kuma shi ne DSS Bauchi, Hassan Abdullahi ya bayyana cewa, manyan makasudin taron su ne a hada kai a yi musayar gogewa tare a shiyyar da samar da mafita.

Ya bayyana garkuwa da mutane, fashi da makami, satar shanu, tayar da kayar baya da kuma ‘yan bangar siyasa a matsayin wasu daga cikin kalubalen tsaro da ake fuskanta a halin yanzu.

Abdullahi ya yabawa gwamnatin jihar Yobe bisa kyakkyawar tarba da aka yi masu a lokacin da suka ziyarci jihar.  Shugaban hukumar ta DSS yayi amfani da dandalin wajen mika godiyarsa ga hukumar raya arewa maso gabas (NEDC) bisa tallafin da take baiwa jami’an tsaro a yankin.

A madadin daukacin majalisun gargajiya na jihar, Mai Martaba Sarkin Fika kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya na Jihar Yobe, Dokta Muhammad Ibn Abali Muhammad Idrissa, a takaice, ya yaba rawar da irin rawar ganin da jami’an tsaron na DSS ke takawa, “Don haka a madadin Sarakuna iyayen kasa majalisa, muna so mu yaba da gagarumin kokari da nasarorin da kuka samu wajen samar da zaman lafiya a jihar, a cikin shekaru 13 da suka gabata, wadda a baya wuraren na karkashin kungiyar Boko Haram amma yanzu an samu kwanciyar hankali matuka.”

Uban Masarautar ya ba da tabbacin cewa “muna tabbatar muku cewa za mu tallafa muku dari bisa dari, mu ba ku hadin kai don samun nasara, muna muku fatan tattaunawa mai amfani”.

Sauran shugabannin hukumomin tsaro da suka fadi albarkacin bakin su sun hada da  ’Yan sanda, Sojoji, NSCDC, FRSC, NIS, NDLEA, NAPTIPP, Mataimakin Shugaban Jami’ar, wakilan NEDC da sauran masu ruwa da tsaki.

Shugaban taron ya gabatar da wata takardar karrmawa  ga ga mai martaba Sarkin Fika kuma shugaban majalisar sarakunan Jihar da kuma wakilin Sarkin Damaturu.

About andiya

Check Also

KADCCIMA ON  ON REVIEW OF ELECTRICITY TARIFF

    Following approval by the Electricity Regulatory Commission (NERC) for the increase of electricity …

Leave a Reply

Your email address will not be published.