Home / Labarai / TSORON ALLAH A ZUCIYA YAKE – SANUSI LAMIDO

TSORON ALLAH A ZUCIYA YAKE – SANUSI LAMIDO

….Hadin kai tsakanin musulmi da Kirista domin zaman lafiya

Daga Imrana Abdullahi,Kaduna arewacin Najeriya

An kara jaddada kira ga daukacin al’ummar duniya baki daya da su ji tsoron Allah matukar tsoro.

Sarkin Kano na sha hudu (14) Sanusi Lamido Sanusi ne wanda kuma shi ne shugaban Darikar Tijjaniyya na Afirka, ya yi wannan kiran a lokacin da yake gabatar da huduba bayan ya jagoranci Sallar Idin Layya a masallacin dandalin Murtala da ke Kaduna.

Sarki Sanusi ya ci gaba da bayanin cewa tsoron Allah a cikin zuciya yake don haka kowa ya kara jajircewa wajen yin Ibada da aiki da tsoron Allah da nufin samun ci gaban al’umma baki daya.

“Yin layya wani abu ne da jama’a ya dace su Sani kowa na yi wa kansa ne a matsayin ibada. Kuma a Sani cewa ba wai Sanya tufafi mai kyau sababbi ne kawai, lamari ne na duk wanda ya gyara tare da kawata zuciyarsa da jin tsoron Allah”.

Ya kara da cewa muna yin addu’ar Allah ya Sanya mu a cikin wadanda ya yi wa tafiya da gafara, yafiya a ranar Arfa, muna kuma addu’ar Allah ya karbi Ibadar wadanda suka samu zuwa aikin Hajji ya kuma dawo da su lafiya.Muna kuma tsokon Allah ya Sanya mu cika da imani muna musulmi idan lokacin mu yazo don haka lallai aji tsoron Allah madaukakin sarki.

Wakilin mu ya kuma samu zantawa da Fasto Yohanna Buru, da ya jagoranci yan uwa Kiristoci da suka halarci masallacin idin domin taya al’ummar musulmi murnar yin Sallar layya a cikin koshin lafiya da nasara.

Fasto Buru ya kuma shaidawa wakilin mu cewa ya halarci wannan masallaci ne domin karfafa dankon zumunci da son a zauna lafiya tsakanin al’ummar musulmi da Kirista baki daya.

“Kamar yadda al’ummar musulmi suke halartar Cocin da nake jagorantar kuma su halarci inda nake a ranar kirsimati duk domin a samu zaman lafiya a tsakanin Juna, wannan ba karamin abin jin dadi bane da alfahari a tsakanin bangarorin biyu baki daya.

Dimbin al’ummar musulmi ne suka halarci Sallar idin babbar Sallah a dandalin tunawa da marigayi Murtala da ke Kaduna.

About andiya

Check Also

Saving Nigeria’s Green Heritage: Environmental Journalist Leads Fight Against Plant Extinction

  Ibrahima Yakubu, a Nigerian environmental journalist, stands as a steadfast guardian of native trees, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.