Home / Labarai / Tumbatsar Kogin Komadigu Ya Jefa Mutanen Garin Haduwa Cikin Mawuyacin Hali

Tumbatsar Kogin Komadigu Ya Jefa Mutanen Garin Haduwa Cikin Mawuyacin Hali

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
A halin da ake ciki ambaliyar ruwa da tumbatsar da babban Kogin nan na Komadugu Yobe a cikin ‘yan kwanakin nan ya yi ya jefa al’ummar garin Gashuwa da ke gabar Kogin cikin mawuyacin hali kasancewar gadaje da dama sun rushe yayin da al’umma da dama ke fakewa a gidajen ‘yan uwa da abokan arziki.
A wannan shekara, Kogin Kumadugu ya yi cika ya batse tare da tumbatsar da ta haifar da mummunan ambaliyar ruwan da ta shafe wasu garuruwa da dama a jihar Yobe, musamman a kananan hukumomin Bade (Gashuwa) da Jakusko- uwa uba garin Gashuwa da kauyukanta, wanda baya ga mamaye kauyukan kuma ya yi wa garin Gashuwa kawanya musamman unguwannin Katuzu, Abujan Amare da wani yanki na Zango da Unguwan Lawan duka a garin na Gashuwa.
Alal misali a halin da ake ciki a yanzu haka unguwar Abujan Amare, ambaliyar ruwan ya rusa sama da gidaje 200, haka kuma ruwan ya rusa fiye da wannan adadin a unguwar Katuzu, tare da mamaye Kasuwar danyen Kaya (gwari), Katuzu Primary, Keasawa Primary da shagunan jama’a da ke bakin Tashar Kuka, duk a cikin garin Gashuwa, Yayin da ambaliyar ruwan ta shafi baki dayan gundumomi 10 dake karamar hukumar Bade, wanda na baya bayan ne su ne garuruwan Gasma da Dagona da ambaliyar ruwan ta mamaye baki daya.
A hannu guda kuma, ambaliyar ruwan ta yi wa qauyuka da garuruwa da daman gaske dukan a kawo wuqa a qaramar hukumar Jakusko; ta rushe gidajen jama’a tare da lamushe amfanin gonakin su- daga ciki akwai garin Girgir, Katamma, Amshi, Guyik, Muguram, Jaba, Jakusko, Dumbari, Gwayo, Dukorel, Lafiya, Bayam, Buduwa, Saminaka, Garin Saje, Dachiya, Zabudum da sauran su.
Sauran sun haxa da Gasamu, Garin-Mallam, Gamajan, Sabon Sara, Garin Kunu, Kurkushe, Adiya, Damasa, Yim, Kazir, Gafala, Arfani, Kambawo da garin Daklam duk a qaramar hukumar Jakusko da ke jihar Yobe.
Bugu da qari kuma, ambaliyar ruwan ta kai Kwanan Koromari (tsakanin Gashu’a zuwa Bayamari) a qaramar hukumar Bursari yayin da take barazana ga qauyuka 10 dake yankin, waxanda suka haxa da Girim Bade, Girim Kanuri, Gilbasu Yamma, Gilbasau Tsakiya, Gilbasau Gabar, Dapso, Garin Kabaju, Guba, Kormari da Kurnawa.
Wasu daga cikin  jama’a wadanda wannan ibtila’in ya shafa, suna ci gaba da bayyana bacin ransu bisa ga halin ko-in-kula da gwamnatocin Tarayya da na jihar ke nuna musu kan halin da suke ciki. Alhaji Kanzi, Mai Unguwar Abujan Amare dake cikin garin Gashuwa, ya ce al’ummar sa suna cikin mawuyacin hali, “Yau sama da kwana 12 muna aikin jingar tare ruwan nan (babu dare babu rana), amma har yanzu bamu taba samun tallafin gwamnati ba illa Shugaban karamar hukumar Bade ya kawo mana gudumawar 20,000, sai Sarkin Bade, ya bamu buhun garin-kwaki biyu da fatun buhuna 500. Wannan shi ne iyakacin tallafin da muka samu a wannan lokacin.”
“A gefe guda kuwa, Shugaban karamar hukumar Bade, Hon. Sanda Kara-Bade ya bayyana cewa, ambaliyar ruwan ta tagayyara rayuwar jama’a, saboda yadda ta rushe gidajen su tare da barnata amfanin gonakin da suka noma. Al’amarin da ya ce dole sai an tashi tsaye wajen tunkarar wannan ibtila’in da suke fuskanta.”
Ya ce, “Saboda haka muna mika sakon godiyarmu ga hukumar kai daukin gaggawa SEMA dangane da tallafin da suka bai wa jama’ar da wannan ibtila’in ya shafa. Amma muna kara mika kokon baranmu al’ummar mu ga Gwamnatin Tarayya da ta jihar Yobe da su kara kaimi tare da tallafa wa jama’a saboda ana cikin mawuyacin halin gaba kura baya sayaki- ambaliyar ruwan ta lalata gidaje da gonakin jama’a kusan ko’ina ka duba a mafi yawan Unguwannin garin duka ruwa ne  kwakkwance.
Hotunan wasu daga cikin Unguwannin garin Gashua da ambaliyar ruwan ta shafa a ‘yan kwanakin nan

About andiya

Check Also

The Daily Hug For Appreciation 2023

The daily hug for 28/11/23 is this appreciation of an echo shared by my dear …

Leave a Reply

Your email address will not be published.