Home / Labarai / Wadansu Yan Bindiga Sun Kashe Mace Mai Ciki, Sun Sace Mijinta A Kaduna

Wadansu Yan Bindiga Sun Kashe Mace Mai Ciki, Sun Sace Mijinta A Kaduna

Imrana Abdullahi

Wadansu masu satar mutane sun sace wata mata mai ciki inda suka kashe ta a ranar Talata da Yamma a Unguwar Rigachikun garin Kaduna.

Wata majiya daga wurin da lamarin ya faru ta shaida mana cewa Matar tare da mijinta an sace su daga gidansu.

Kamar yadda majiyarmu ta shaida mana cewa a lokacin da masu satar mutanen suka zo da jami’an tsaro suka yi masu kawanya aka kuma fara masayar wuta a kokarin da suke yi na kubutar da wadanda aka sace.

Rundunar Yan Sanda ta kasa reshen Jihar Kaduna ta bakin mai magana da yawun rundunar ASP Muhammad Jalige ya zuwa lokacin rubuta wannan labarin mun yi kokarin magana da shi a waya.

Amma majiyarmu ta ce: “Maharan sun kawo hari gidanne suka kuma tafi da su, sai jami’an tsaro suka bi yawunsu a lokacin da ake masayar wuta sai maharan suka harbi matar nan da nan aka wuce da ita asibiti ta kuma mutu a asibitin”.

“Matar dai na da ciki kuma ta kusa haihuwa kafin faruwar wannan lamari na bacin rai. Tuni dai aka yi Jana’izarta Lamar yadda addinin musulunci ya shimfida”.

About andiya

Check Also

Gwamna Dauda Lawal Ya Kaddamar Da Manyan Ayyuka A Bakura Da Maradun

A ci gaba da gudanar da bukukuwan cika shekara ɗaya a karagar mulkin jihar Zamfara, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.