Home / News / Wasu Jiga Jigan PDP Sun Yi Bitar Zaben 2019

Wasu Jiga Jigan PDP Sun Yi Bitar Zaben 2019

Wasu Jiga Jigan PDP Sun Yi Bitar Zaben 2019

Imrana Abdullahi
Wadansu Jiga Jigan jam’iyyar PDP da ta kwashe shekaru 16 ta na mulki a Nijeriya sun yi taron bitar zaben shekarar 2019 taron dai an yi shi ne karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan.
Shi dai kwamitin bitar zaben 2019 da yayan jam’iyyar PDP suka yi an yi taron ne a karkashin tsohon shugaban kasar da muka bambanci sunansa.

Sauran mahalarta taron sun hada da shugaban Talakawa Dokta Sule Lamido CON, Gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad, tsohon Gwamnan Neja Mu’azu Babangida Aliyu CON, Babban lauyan Nijeriya Tanimu Turaki, Dokta Emmanuel Agbo mataimakin Sakatare na kasa da Sakataren kwamitin Cif Bola Olu-Ojo a gidansa da ke unguwar Maitama cikin birnin  Abuja.

Mun dai samu wannan sanarwar taron ne daga Mansur Ahmed mai taimakawa tsohon Gwamna Sule Lamido a kan harkokin kafafen dandalin Sada zumunta na zamani, a ranar 26 ha watan Satumba, 2020.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.