Home / Labarai / Watan Ramadan: Dan Majalisa Abdulkarim Mai Kero Ya bukaci A Yi Wa Kasa Addu’a

Watan Ramadan: Dan Majalisa Abdulkarim Mai Kero Ya bukaci A Yi Wa Kasa Addu’a

…. ya raba Shinkafa buhu dubu 3000 a Maza’barsa 
Dan Majalisa Mai Wakiltan Kaduna ta Kudu a Majalisar Wakilai ta taraiya da ke Abuja Honarabul Abdulkarim Hussaini Ahmad da ake yi wa lakabi da Mai Kero ya ta ya al’ummar musulmi murnan shigowar Watan Azumin  Ramadan mai Alfarma a 1445.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa mai dauke da sa hannun Sharifudeen Ibrahim Muhammad (Dan Jarida) Me Magana da yawun Dan Majalisa Mai Wakiltan Kaduna ta Kudu a Majalisar Wakilai ta taraiya da ke Abuja da aka rabawa manema labarai a Kaduna.
Honarabu Abdulkarim Hussaini ya hori al’ummar musulmi da suka fito daga Maza’bar Kaduna ta Kudu da su yi amfani da wannan damar na Watan Ramadan don aikata kyawawan aiyuka  kamar yadda addinin musulunci ya ko yar.
A jawabin da me magana da yawun Dan Majalisan Sharifudeen Ibrahim Muhammad (Dan Jarida) ya fitar a ranar Litani, Honarabu Abdulkarim Mai Kero ya bukaci al’ummar musulmi da su dukufa wajen yi wa Kasa addu’a duba da irin yadda tattalin arzikin-Kasa ke ci gaba da tabarbarewa, Wanda hakan ya Sanya jama’ar  kasa cikin wani matsi.
Da yake yaban yadda rabon shinkafa fiye da buhu 3000 ya gudana karkashin Babban Mai taimaka masa, Honarabul Hassan Ya’u Musa Kura tare da Mai taimaka masa na musamman, Honarabul Auwal Alhassan Gwadabe, Dan Majalisa Mai Kero, ya roki   al’ummar musulmi da su yi masa Addu’ar kammalawa lafiya tare da Samar da wakilci nagari.
Bugu da Kari, Honorabul Kero, ya yi addu’ar Allah ya bai wa Maza’bar Kaduna ta Kudu, Jihar Kaduna tare da Kasa Baki daya Zaman Lafiya tare ci gaba mai dorewa.
Da yake raba wa al’ummar Maza’barsa fiye da buhun shinkafa dubu uku Domin rage radadin da mutane ke ciki a ofishisa da ke Barnawa, Honarabul Hassan Ya’u Musa Kura, ya ce gudun cinkoso yasa suka raba rabon gida uku,  mazabu uku da ke Kaduna ta Kudu; Mekera, Tudun Wada da Unguwan Sanusi, sai Kuma a matakin Gundumomi da unguwanni.

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.