Home / Uncategorized / Yakamata Matawalle Da Gwamna Dauda Lawal Su Hada Kansu – Bashir Nafaru

Yakamata Matawalle Da Gwamna Dauda Lawal Su Hada Kansu – Bashir Nafaru

Daga Imrana Abdullahi

An yi kira ga tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ministan kasa a ma’aikatar tsaro Muhammad Bello Matawalle da kuma Gwamna mai ci a yanzu Dokta Dauda Lawal da su kara hada kansu ta yadda za su yi wa Jihar Zamfara aikin raya kasa domin jama’a su amfana.

Alhaji Bashir Nafaru Talatar Mafara ne ya yi wannan kiran a cikin wani sakon da ya aikewa wakilinmu.
Bashir Nafaru ya ci gaba da bayanin cewa hakika samun hadin kan wadannan mutane guda biyu ne abin da ake nema a koda yaushe a duk fadin jihar Zamfara baki daya saboda idan hadin kan ya samu za a ga gagarumin ci gaban da kowa ke bukata.
“Kasancewar dukkansu sun yi aiki a matsayin Gwamna a Jihar Zamfara sun san abin da jihar ke ciki kuma a halin yanzu Allah ya ba su iko ko wani matsayi na shugabanci a lokacin da talakawa ke neman agaji da neman taimako na rayukansu da dukiyaoyinsu don haka wadannan Gwarazan shugabanni su yi kokari su hada kansu domin a samu mafita a jihar Zamfara shi ya sa muke son su hada kansu a taimaki al’ummar Jihar Zamfara ta fuskar tsaro da aikin yi da Taki tare da abinci komai ya dai dai ta a samu sukuni

About andiya

Check Also

GWAMNA LAWAL YA RABA MOTOCIN AIKI 140 GA JAMI’AN TSARON JIHAR ZAMFARA, TARE DA ƘADDAMAR DA BAS-BAS NA SUFURI MALLAKIN GWAMNATIN JIHAR.

  Gwamna Dauda Lawal ya raba wasu motocin zirga-zirga ga rukunonin jami’an tsaron da ke …

Leave a Reply

Your email address will not be published.