Home / Labarai / YAN ASALIN SHINKAFI MAZAUNAN KADUNA SUN KAI WA SULEIMAN SHINKAFI ZIYARA A KADUNA

YAN ASALIN SHINKAFI MAZAUNAN KADUNA SUN KAI WA SULEIMAN SHINKAFI ZIYARA A KADUNA

 

 

 

IMRANA ABDULLAHI DAGA KADUNA

 

Yayan kungiyar yan asalin karamar hukumar Shinkafi mazauna Kaduna sun kaiwa Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ziyarar ban girma domin kara karfafa dankon zumunci.

 

Sa yake gabatar da jawabi  Shugaban Kungiyar Hassan Sa’adu, cewa ya yi sun yi wannan shawara ne na zuwa su ziyarci mai ba Gwamnan Jihar Zamfara shawara a kan harkar hulda da kasashen waje Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi domin kara karfafa dankon zumunci da kuma neman taimakon Gwamnati a fannoni daban daban ta yadda yaya kungiyar za su samu romon Dimokuradiyya.

 

“Muna yin kokarin tara kudi naira dari a kowa ne sati domin taimakawa jama’ar da ke cikin wannan kungiyar, naira Hamsin a saka cikin asusun kungiya naira Hamsin kuma an ware ta domin aiwatar da muhimman ayyukan ciyar da yayan kungiyar gaba”, Inji Hassan.

Yayan kungiyar yan asalin karamar hukumar Shinkafi mazaunan Kaduna sun bayyana cewa babban dalilin da ya sa suka kawo wannan ziyarar shi ne domin kara karfafa dankon zumunci tsakaninsu da mai ba Gwamnan Jihar Zamfara shawara a kan hulda da kasashen waje kasancewarsa mutumin da kowa ya san shi saboda Dokta Suleiman mutum ne mai kokarin kare martaba da mutuncin jama’ar Najeriya baki daya.

Kungiyar nan na kokarin taimakawa yayanta ta fannoni daban daban da suka hada da yi wa wasu jama’a dinki a lokutan Sallah da dai sauran abubuwa da yawa.

 

A nasa jawabin Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, cewa ya yi hakika farin cikin da yake da wannan tsarin kungiyar abin farin ciki ne a gare shi ya hada kansa da duk wani dan asalin karamar hukumar Shinkafi da Jihar Zamfara baki daya.

Ya ce zamanku nan duk abin da kuka samu za ku kwasa ku kai shi gida abin alfahari ne.

“Akwai basussukan da za a ba yan asalin Jihar Zamfara domin yin jari a ko’ina suke

Ya kara da cewa lokaci ya yi da a duk inda mutum yake zai taimakawa Iiharsa da karamar hukumar Shinkafi.

Ya kuma yi kira ga yayan kungiyar da su zama jakadu na kwarai domin kare martaba da mutuncin karamar hukumar Shinkafi da Jihar Zamfara baki daya.

Muna kara yin kira a gare ku da ku tabbatar kun ci gaba da zama tsintsiya madaurinki daya, har lokacin da za a yi zabe ku ta fi guda Jihar Zamfara ku Jefa kuri’arku

” Zan shiga cikin wannan kungiya in kare martaba da mutuncin jama’a tun a da can balantana kuma a yanzu, duk wani da yake kokarin ce maku wai ku ba yan Jiha ba ne ba wannan magana dan Najeriya duk dan Najeriya ne a ko’ina ya samu kansa

Zan zamar maku Garkuwa a kowa ne lokaci za mu tabbatar an dauko ku kun shiga tsarin yin zabe mai zuwa.

 

 

 

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.