Home / News / Tsohon Shugaban PDP, Dimbin Magoya Bayansa Fiye Da  1051 Sun Koma APC A Yobe

Tsohon Shugaban PDP, Dimbin Magoya Bayansa Fiye Da  1051 Sun Koma APC A Yobe

 

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

 

 

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP a Jihar Yobe, Alhaji Abbagana Tata, tare da magoya bayan jam’iyyar fiye da 1,051 daga shiyyoyin jihar, sun fice daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar APC mai mulkin Jihar.

 

 

Tsohon jigo a jam’iyyar PDP ya ce shi da dubban ‘yan jam’iyyar PDP sun shiga jam’iyyar APC ne domin nuna godiya ga gagarumin nasarorin da gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni ta samu.

“Mun shiga jam’iyyar APC ne domin mu marawa gwamnatin Buni baya domin gina jiharmu mai daraja, za mu marawa gwamnati da jam’iyyar baya a kokarin ciyar da jihar Yobe gaba.

 

 

“Ina so in tabbatar da biyayyarmu ga mai girma Gwamna Mai Mala Buni, da shugabancin jam’iyyar APC da kuma gwamnatin jihar Yobe,” Abbagana ya tabbatar.

Da yake karbar tsoffin jiga-jigan PDP, Gwamna Buni, ya yabawa wadanda suka sauya sheka bisa jajircewa da kaunar da suke yi wa jihar.

 

 

“Na yi farin ciki matuka da sauya sheka da kishin kasa da kuma godiya ga gwamnatin APC da kuke ciki yanzu,” in ji shi.

A cewar Gwamnan, Abbagana Tata dan siyasa ne mai bin ka’ida kuma mai kishin kasa da jihar sa wanda  abin duniya ba shi ne gaba sa ba, ya bar jam’iyyarsa ga kan haka ya bar tsuhuwar Jam’iyyar sa ya zuwa Jam’iyyar mu mai adalci.

 

 

“Saboda haka ina godiya da cewa irin wadannan ‘yan siyasa masu kishin kasa sun gamsu da irin nasarorin da muka samu na shiga jam’iyyar mu ta APC.”

“Mun gudanar da manufofi da shirye-shirye na gaba don samar da makoma mai wadata ga mutanenmu.”

 

 

“Za mu ci gaba da kasancewa masu dogaro da kai don inganta rayuwar mutanenmu nagari” Gwamna Buni ya tabbatar.”

Ya kuma yi kira ga ‘yan jam’iyyar da su kara bude wa wadanda suka fice daga wasu jam’iyyu kofa zuwa APC.

 

“Muna da isasshen sarari don ɗaukar kowa da kowa da dama daidai,” in ji shi.

Gwamnan ya ce daga yanzu sabbin ‘ya’yan jam’iyyar za su samu daidaito da dama kamar tsofaffin ‘ya’yan jam’iyyar.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.