Home / Big News / Yan Bindiga Sun Halaka Mutane 7 A Igabi Da Kajuru

Yan Bindiga Sun Halaka Mutane 7 A Igabi Da Kajuru

Yan Bindiga Sun Halaka Mutane 7A Igabi Da Kajuru

Mustapha Imrana Abdullahi

Rahotannin da muke samu daga Jihar Kaduna arewacin tarayyar Nigeriya na cewa wadansu yan bindiga da suka kai wasu hare hare sun halakar da mutane Bakwai (7) a kananan hukumomin Igabi da kuma Kajuru duk a cikin Jihar Kaduna.

Kamar dai yadda sanarwar da kwamishinan kula da harkokin cikin gida da tsaro na Iihar kaduna Malam Samuel Aruwan ya fitar a yau Lahadi Gwamnatin ta tabbatar da samun rahotanni daga jami’an tsaro kan cewa yan bindiga sun kai hari a kauyen Kajinjiri karamar hukumar Igabi inda suka kashe mutane biyu masu suna kamar haka, Ibrahim Rabiu da Abdulrahman Mohammad.

Sai kuma wani mai suna Kamal Murtala da ya samu raunuka sakamakon harbin bindiga an nan yanzu haka ana duba lafiyarsa a wani guri kusa da su.

Hakazalika a kauyen Rago duk a karamar hukumar Igabi, yan bindiga nan ma sun kashe mutane biyu da sunansu kamar haka Alhaji Ibrahim Iro da Muhmadu Rabi’u.

Sai kuma takardar da Samuel Aruwan ya Sanya wa hannu ta ci gaba da cewa a Tashar Katuru da ke karamar hukumar Kajuru nan ma an kai hari an kuma kashe mutane masu suna  Michael Shadari, Clement Aura Bili and Danlami Shaban.

Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana rashin jindadinsa da samun wannan rahoton inda ya yi wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu ta’aziyya tare da samun ragamar Allah, shi kuma wanda ya samu rauni da fatan Allah ya bashi lafiya cikin gaggawa.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.