Home / Big News / Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Goma A Zangon Kataf, Chikun

Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Goma A Zangon Kataf, Chikun

Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Goma A Zangon Kataf, Chikun
Mustapha Imrana Abdullahi
Al’ummar kananan hukumomin Zangon Kataf da Chikun sun samu kansu cikin wani irin yanayi sakamakon kisan da aka yi wa wadansu mutane Goma.
Jami’an tsaron Sojoji ne da wasu hukumomin tsaro suka bayar da rahoton kashe mutanen guda Goma yan asalin kananan hukumomin Zangon Kataf da Chikun duk a Jihar Kaduna.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun kwamishinan ma’aikatar tsaro da al’amuran cikin gida Malam Samuel Aruwan.
Kamar yadda sanarwar ta ce lamarin dai ya faru ne a kauyen Kurmin Gandu a karamar hukumar Zangon Kataf  inda maharan suka kashe mutane biyar, da aka samu sunayensu kamar haka.
– Ishaya Aboi
– Regina Ishaya
– Goodluck Dauda
– Joseph Adamu
– Hassan Joseph
Bugu da kari in ji sanarwar an kona gidaje 10 , Baburan hawa biyu da Buhuna 50 na Jinja duk an Kone su baki daya.
Wasu kuma Manoman rani sun yi asarar injunansu na ban ruwa da sauran wadansu kayayyaki a yankin Zango.
Wadansu kuma da suka tsira da rayukansu daga garin suna can asibiti suna murmurewa, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike a halin yanzu, kuma dukkan bayanan da aka samu danga ne da lamarin za a ga ya wa jama’a yadda lamarin yake.
Lamarin dai ya dauki jami’an Sojoji awanni Karin shawo kan matsalar.
Hakazalika rahotanni daga jami’an tsaro sun bayyana cewa mahara sun kai hari a kauyen Sabuwar Gayan da ke karamar hukumar Chikun, sun kuma kashe mutane hudu, masu suna kamar haka.
– Ashahabu Abubakar
– Ado Rilwanu
– Sabo Iliya
– Mannaseh Matthias Danjuma
Jami’an tsaron “Thunder strike” na can na neman wasu daga cikin maharan da ake zaton sun shige maboyarsu tare da raunuka harbin harsashi.
Wadansu maharan dai sun kai hari a unguwar Turai a karamar hukumar Chikun inda suka kashe wani mai suna Ayuba Waziri.

About andiya

Check Also

Sokoto state government dethrones 15 traditional leaders, four others being investigated for various offences

  By S. Adamu, Sokoto Fifteen Sokoto traditional leaders have been dethroned by the Sokoto …

Leave a Reply

Your email address will not be published.