Home / Big News / Yan Bindiga Sun Kashe Yan Sa Kai 17 A Neja

Yan Bindiga Sun Kashe Yan Sa Kai 17 A Neja

Imrana Abdullahi

Rahotannin da muke samu daga Jihar Neja a arewacin tarayyar Nijeriya bayanin cewa akalla mutane 17 masu ayyukan sa kai domin tabbatar da tsaro aka halaka

Kamar dai yadda rahotannin suka tabbatar cewa lamarin dai ya faru ne a Dukku da ke karamar hukumar Rijau a lokacin da suke kokarin hana yan bindigar aikata ayyukan nasu.

Wani shaidan gani da ido ya shaidawa majiyarmu a wata tattaunawar da suka yi ta wayar salula a Minna cewa yan bindigar da suka kai Dari da Ashirin suna a kan Babura 40 ne lokacin da lamarin ya faru.

Kwamishinan yada labarai Alhaji Muhammad Sani Idris ya tabbatar da faruwar lamarin inda a lokacin yake cewa ana kokarin tabbatar da yawan wadanda lamarin ya shafa.

Alhaji Muhammad Idris ya ce tuni Gwamnatin Jihar Neja ta dauki matakan tsaro

Ya ce koda yake ba wani abin da za a fito fili a rika bayaninsa bane a bainar jama’a, amma za su rika gayawa manema labarai irin nasarar da ake samu a game da lamarin na tsaro.

Kwamishinan ya ci gaba da cewa Gwamna ya amince da shugaban ma’aikatan gidan Gwamnati Alhaji Ibrahim Balarabe Balarabe wakilci Gwamna Abubakar Sani Bello domin kaiwa iyalan da lamarin ya rutsa da Mutanensu ziyarar jaje da Ta’aziyya a Kagara karamar hukumar Rafi.

Masu aikin as kan sun

kashe yan bindigar mutane biyu a lokacin musayar wutar da suka yi kuma gawarsu na can tare da yan bindigar da suka ce ba za su mika su ba domin yi masu jana’iza

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan Jihar Neja ASP Wasi’u Abiodun an kasa samunsa domin tofa albarkacin bakinsa game da lamarin.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.