Home / Labarai / Yan bindiga Sun Watsa Garuruwa Sama Da 30 A Kasar Birnin – Sarkin Birnin Gwari

Yan bindiga Sun Watsa Garuruwa Sama Da 30 A Kasar Birnin – Sarkin Birnin Gwari

Yan bindiga Sun Watsa Garuruwa Sama Da 30 A Kasar Birnin – Sarkin Birnin Gwari
Mustapha Imrana Abdullahi
Mai Martaba Sarkin Birnin Gwari Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II ya bayyana irin yadda wadansu garuruwa a karkashin Masarautarsa da suka kai sama da Talatin (30) a halin yanzu ba kowa a ciki saboda dukkan mutanen garuruwan sun kama gabansu, sakamakon aikin yan bindiga.
Mai Martaba Sarkin Birnin Gwari ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin shugabanni da yayan kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) reshen Jihar Kaduna da suka kai  masa ziyarar jajen abin da ya faru karkashin jagorancin shugaba na Jiha Lawal Umar Mayere.
Mai Martaba Sarkin Birnin Gwari ya ce hakika mutanen kasar Birnin Gwari masu son zaman lafiya ne kuma su na da hakuri kwarai matuka da gaske domin wasu mutane ne suka same su a wurin amma a yanzu duk sun tsiyata mutanen da ke suka kasance yan asalin wannan wuri ta hanyar sace su sai sun biya kudin fansa.
” Wanda wannan kudin fansa ana sayar da Gonaki ne da kadarorin da mutum, yan uwa da abokan arziki suka mallaka domin a biya kudin fansar wanda aka sace, kuma matsalar ta haifarwa mutanen kasar Birnin Gwari rashin aiwatar da ayyukan Gonakinsu da hakan ya haifar da dimbin matsaloli ga jama’a da dama”, inji Sarkin.
Ya kara da cewa sama da shekaru 20 babu wani ci gaban da aka kawo a kasar Birnin Gwari, “hatta wannan jami’ar da aka shirya yi a Manchok sai da ya yi magana da kowa duk kowa ya  amince amma haka kawai sai aka ce saboda halin rashin tsaro ba za a yi ta a wannan wurin ba sai aka kai ta Manchok.
Mai martaba ya ci gaba da bayanin cewa a dai dai wurin da aka kaiwa ayarin motarsa hari a wurin ne aka kashe dan uwar matarsa, kuma a nan ne aka kashe Gogarin Sarkin Yawuri da zai koma gida bayan kammala wani taro a Kaduna, a dai wurin ne aka kaiwa jerin Gwanon motocin shugaban karamar hukumar Birnin Gwari hari har aka kona mota don haka wannan wuri an dade ana ta’asa a wurin.
” Ni ba na son ayi wani sansanin yan gudun hijira ne saboda haka ne na gayawa dukkan mutanen da aka hana zama a garuruwansu da Gonakinsu cewa kowa ya na da yan uwa to ayi hakuri kowa ya rungumi dan uwansa a zauna tare ayi ta addu’a har Allah ya magance lamarin”.
Hakika muna yi wa Gwamnati godiya a kan irin kokarin da suke yi a fannin tsaro domin shi ya san suna kokari a kan lamarin, ya bayar da misalin sansanin sojojin sama da ya bayar da Gonarsa aka ajiye su tare da sojojin saman Kundun bala da aka ajiye wanda hakan ya taimaka masu kwarai matuka.
Hakika addu’a ita ce abin yi domin idan aka yi duba sosai za a ga cewa akwai abin da aka yi wa Allah wanda sanadiyyar hakan abubuwa suke faruwa kamar yadda suke a halin yanzu don haka a dukufa da yin addu’a.
Da yake jawabi Lawal Umar Mayere ya bayyana cewa sun kai wannan ziyara ne domin jajantawa Mai martaba Sarkin Birnin Gwari Malam Zubairu Jibril Mai Gwari II bisa abin da ya faru na kaiwa motocinsa hari a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna.
Mayere, ya ci gaba da cewa su na addu’ar Allah ya  kare faruwar irin wannan lamarin a nan gaba ya kuma bayar da zaman lafiya na ci gaban kasa.

About andiya

Check Also

APC SOKOTO FLAGS OFF STATE-WIDE CAMPAIGN IN WAMAKKO LG, UNVEILS 8-POINT AGENDA

  The All Progressives Congress (APC), Sokoto State chapter on Wednesday flagged off its state-wide …

Leave a Reply

Your email address will not be published.