Home / News / YAN MAJALISA 360 BABU KAMAR ABBAS TAJUDDEEN – KWAMARED MAUDE ZARIYA

YAN MAJALISA 360 BABU KAMAR ABBAS TAJUDDEEN – KWAMARED MAUDE ZARIYA

Daga Imrana Abdullahi, Kaduna

Kwamared Maude Zariya ya bayyana cewa ba tare da fariya ba a duk cikin yan majalisar wakilai na tarayyar Najeriya guda dari 360 babu kamar Dokta Abbas Tajuddeen dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar Zariya.

Hakika ina fadin wannan maganar ne ba tare da fariya ba sai domin kawai Abbas Tajuddeen mutum ne cikakke kamilin mutum mai hakuri tare da hangen nesa ga kuma son jama’a koda yaushe.

Kwamared Maude Zariya ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da wakilin mu a garin Kaduna.

Maude Zariya ya ci gaba da bayanin cewa in dai wanda zai taimakawa Najeriya ne ta samu ci gaban da kowa ke bukata hakika babu kamar Abbas Tajuddeen, a cikin majalisar wakilai ta kasa.

” Saboda mutum ne mai gaskiya mai cika alkawari domin duk inda aka yi alkawari da shi sai ya cika, kuma a batun tafiyar APC shi kadai ne mutumin da ya rike lardin Zazzau inda ya yi aiki tukuru ba tare da samun wata tangarda ba. Ya kuma biya wa mutane kudin duba lafiya har aka yi masu ofireshin ( Fida) aka cirewa mutane dubu Tara (9000) cututtuka daban daban kyauta, an kuma yi aikin ne a asibitocin Dokta Bello da ABU Shika da na Tudun wada Zariya”.

“Kai akwai wani da aka yi wa aiki har aka zo aka gaya Mani cewa da kansa mutum ya ce  a lokacin ba shi da kudi yaje wani asibiti aka ce masa sai ya kawo naira dubu dari biyu da Hamsin. Sai ga shi bai ta ba ganin Abbas Tajuddeen ba an yi masa aikin nan kyauta to irin su fa mutane dubu Tara ne aka yi wa wannan aikin kala daban daban don haka mu muna yi wa Allah godiya da ya ba mu wannan bawan Allah mai son taimakawa jama’a”.

Ana yin haka ina kuma ga ya zama shugaban majalisar wakilai ta kasa.

Kuma Dokta Abbas ne dan majalisar da a duk yankin nan na mu ya fi kowa ne dan majalisa gabatar da Kudirori a gaban majalisa da har a ciki an samu guda 22 sun samu amincewar majalisar wakilai ta kasa, wanda daman abin da suka je yi kenan a majalisar.

Kwamared Maude Zariya ya kara da yin jinjina ga zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa irin yadda ya yi hangen nesa ya zabi Dokta Abbas Tajudden daga Jihar Kaduna kuma wanda ya fito daga cikin garin Zariya, dan asalin Kwarbai Bamallen asali gaba da baya.

Haka kuma Gwamna Malam Nasiru Ahmad El – rufa’i da suka dauki wannan matsayin na kujerar shugaban majalisar wakilai ga mutum mai gaskiya da rikon Amana Dokta Abbas Tajuddeen.

Kwamared Maude Zariya ya kuma yi kira ga daukacin yan majalisa musamman yayan jam’iyyar APC da su tabbatar sun bi jam’iyya a kan duk abin da take son ayi domin kowa na son Jam’iyyarsa ba mai son ta fadi indai asalin dan jam’iyya ne mai kishi.

“Jam’iyya ta ce Abbas Tajuddeen, shugaban kasa zababben mai jiran rantsuwar kama aiki ya ce Abbas Tajuddeen, kunga ba abin da ya rage sai kawai a marawa jam’iyya baya domin duk abin da shugabanni suka tsara ba za su yi na rashin adalci ba sai abin da kasa za ta ci gaba za su aiwatar a koda yaushe.

” Ko a nan Jihar Kaduna muna yi wa Malam Nasiru godiya sakamakon yadda ya dauko Uba Sani da zai Dora a kan irin ayyukan alkairin da Malam Nasiru ke aiwatarwa a Jihar Kaduna, an canza Kaduna baki daya kuma da Allah yasa Malam Nasiru ya samu wadatattun kudi tun lokacin da ya zama Gwamna ni Kwamared Maude Zariya na tabbata da sai ya mayar da Kaduna wata karamar Landan saboda ayyuka.

Saboda haka nake yin kira ga yan majalisar wakilai a kan lallai su tabbatar da cikakken hadin kansu da goyon baya ga Dokta Abbas Tajuddeen su zabe shi shugaban majalisar wakilai karo na Goma da za a kafa a Najeriya domin kasar mu ta yi kyau al’amura su inganta.

Dokta Abbas Tajuddeen Iyan Zazzau da ya san darajar jama’a yake ganin girma kowa a matsayinsa na mai sarauta da ko can kowa nasa ne ina ga ya zama shugaban majalisar wakilai ta tarayyar Najeriya ai jama’a za su samu dadi kan dadi ne kawai a duk fadin kasar baki daya.

About andiya

Check Also

MAY DAY 2024: GOV. DAUDA LAWAL RENEWS COMMITMENT TO IMPROVE WELFARE OF ZAMFARA WORKERS

By; Imrana Abdullahi Governor Dauda Lawal reiterated his administration’s commitment to improving the well-being of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.