Related Articles
MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
Jagororin kwamitin shirya zaben dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC domin tsayawa zaben shekarar 2023 sun bayyana cewa ya zuwa yanzu yan takara Goma sha hudu ne 14 za su fafata a zaben.
Bayan da aka samu yawan yan takara mutum Tara da suka bayyana janyewarsu wasu suka bayyana goyon bayan su ga dan takara Bola Ahmad Tinubu inda wani daga cikin yan takarar ya bayyana goyon bayansa ga mataimakin shugaban kasa Farfesa Yomi Osinbajo.
Wannan janyewar ta biyo bayan damar da aka ba yan takarar ne su yi wa jama’ar da suka halarci taron da kuma duniya bayani.
A cikinsu had da wata yar takara mace guda daya da ke takarar shugaban kasa inda ta bayyana cewa ta janye ta bayyana goyon bayan ta ga dan takara Cif Bola Ahmed Tinubu, ta ce ta na matukar nuna kauna da Soyayya ga daukacin yan Najeriya.