Home / Labarai / AN GARGADI MASU KOKARIN MATSAWA MASU ZABEN DAN TAKARA

AN GARGADI MASU KOKARIN MATSAWA MASU ZABEN DAN TAKARA

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
Kwamitin shirya zaben dan takarar da zai tsayawa jam’iyyar APC takarar shugaban kasa a tarayyar Najeriya sun bayyana gargadi karara ga masu kokarin matsawa masu zaben dan takara su rubuta sunan da suke bukata sabanin irin tanaje tanajen zaben ya tanadar.
A lokacin da aka fara gudanar da zaben dan takara da misalin bayan karfe daya na daren Laraba sai yan kwamitin suka bayyana cewa akwai wasu da ke kokarin matsawa masu zaben sai sun zabe wani dan takarar da ba son ran su ba.
“Mun samu labarin cewa akwai wasu da ke matsawa yan takara sai sun zabi wani dan takara, saboda haka duk wanda muka samu wani na matsa masa ya zabi dan takara to ya hanzarta kai kukansa ga kwamitin shirya zaben domin daukar matakan da suka dace”.

About andiya

Check Also

Kaduna Church Leaders Visit Imams at Eid Praying Ground to Promote Peace, Love, and Religious Tolerance

    In a remarkable demonstration of interfaith harmony, Pastor (Dr.) Yohanna Buru, a Christian …

Leave a Reply

Your email address will not be published.