Home / Big News / Za A Ci gaba Da Rufe Jihar Kaduna Baki Day

Za A Ci gaba Da Rufe Jihar Kaduna Baki Day

Daga Imrana kaduna
Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i ta bayyana cewa in har mutane basa kiyayewa da dokar hana fita da aka kafa za ta toshe kafar kwanaki biyun da ake samu a lokacin dokar.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da Gwamnatin ta fitar mai dauke da sa hannun Muyiwa Adekeye. Inda takardar ta fayyace karara cewa Gwamnati ta lura da wadansu mutane na kokarin kin bin dokar da kaa kafa domin kiyaye lafiya da dukiyar jama’a baki daya.
Gwamnatin Jihar kaduna dai ta kafa dokar hana fita ne tsawon Dare da rana domin daukar matakin hana yaduwar kwayar cutar Korona Bairus da ta addabi duniya baki daya a halin yanzu.
Amma da wakilinmu yaji ta bakin shugaban jam’iyyar Lebo kuma shugaban gamayyar kungiyar jam’iyyun siyasa na Jihar kaduna Alhaji Ibrahim Umar Taba Mai Rakumi cewa ya yi su dai suna cikin gidajensu kuma duk abin da Gwamnatin ta ce suyi za su yi domin hakan manuface ta kiyaye lafiyar al’umma baki daya.
Gwamnatin Jihar dai na kokarin cika alkawarin da ta yi wa jama’a na bi gida gida domin Raba masu kayan abinci da ya samu domin saukaka wa mutane halin da ake ciki.

About andiya

Check Also

BANDITRY: WE TOOK THE WAR TO THE NEXT LEVEL- DIKKO RADDA

By Lawal Sa’idu in Katsina In an effort to bring an end to BANDITRY and …

Leave a Reply

Your email address will not be published.