DAGA IMRANA ABDULLAHI
Bayanan da muke samu daga Jihar katsina da ke Arewa ta Yammacin tarayyar Najeriya na cewa tuni har an kammala shirye-shiryen fara aikin tantance ma’aikata da tantancewa da aka shirya gudanarwa gobe litinin, Goma ga watan Yuli na wannan shekara.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun Hassan Muhammad Tukur Kakakin kwamiti gudanar da binciken da tantancewa.
An gudanar da taron share fage kan yadda za a gudanar da atisayen a wannan Lahadin, wanda shugaban kwamitin Alhaji Rabi’u Abdu Ruma,ya jagoranta tare da halartar mambobin kwamitin guda 19.
Shugaban ya sanar da cewa, Ma’aikatun Ma’aikatu goma sha biyar da Ma’aikatun, hukumomin (MDAs) ne za a fara tantance a ranar farko ta fara aikin.
Alhaji Rabi’u Ruma ya lissafa MDAs da abin ya shafa sun hada da KTSTA, SEMA, Mathematical centre, MOWH&T, FASCOT, KASSROTA da kuma ma’aikatar wasanni da ci gaban al’umma ta Jihar.
Sauran ya ce sun hada da hukumar wasanni, hukumar ruwa, hukumar kula da harkokin da kimiya da fasaha, ya kuma ce sauran sun hada da madaba’ar Gwamnatin Jihar, sai hukumar yalbijin ta jiha KTTV, da hukumar kula da tsaftace muhalli (SEPA).
Alhaji Rabi’u Ruma ya bayyana cewa za a fara atisayen ne da karfe Goma na safe kuma za a rufe da karfe biyar na yamma.
Shugaban ya bukaci Daraktocin gudanarwa da kayayyaki-DAS da su tabbatar da bin ka’idojin kwamitin kamar yadda aka tura a wasikunsu daga kwamitin.