Home / Ilimi / Za A Fara Koyar Da Dalibai Ta Rediyo A Kaduna

Za A Fara Koyar Da Dalibai Ta Rediyo A Kaduna

Daga Imrana Abdullahi kaduna
A cikin wata sanarwar da ma’aikatar ilimin Jihar Kaduna ta fitar na cewa tuni sun kammala shirin fara koyar da yara dalibai musamman wadanda suke aji uku na babbar sakandare cewa za a fara koyar da su darussa ta hanyar amfani da Rediyon Jihar Kaduna a ranar Litinin wato gobe, 6 ha watan Afrilu, 2020.
Ma aikatar ilimin na kira ga dukkan dalibai su yi amfani da wannan damar su koyi karatu suna cikin gidajensu.
Sanarwar ta ci gaba da bayanin cewa za a fara yin amfani da kafar yada labarai ta rediyon Jihar Kaduna KSMC don haka ake umartar daliban da su saurari gidan rediyon domin jin yadda jadawalin shirin karatun kowane darasi zai kasance a kullum, ana kuma ci gaba da shirin zai fadada zuwa ga wadansu kafafen rediyon nan gaba.

About andiya

Check Also

NASCON grows turnover by 37%, assures Shareholders of Continuous Growth, Value Creation

NASCON Allied Industries Plc has assured its shareholders of continuous growth and value creation in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.