Home / Ilimi / Za A Koyar Da Yan Firamare Ta Rediyo A Kaduna

Za A Koyar Da Yan Firamare Ta Rediyo A Kaduna

A kokarin ganin an ci gaba da bayar da ilimi ga yara a makarantun Firamare da ke Jihar Kaduna hukumar samar da ilimin bai daya ta Jihar ta fitar da tsarin jadawalin koyar da daliban Firamare da kafar yada Labaran rediyon Jihar Kaduna.

Wannan jadawalin koyar da daliban na dauke ne da sa hannun shugaban hukumar Alhaji Abdullahi Sani, da aka yi bayani Dalla dalla yadda tsarin karantarwa da Rediyon zai kasance domin kowa ya zama cikin koshin lafiya da ci gaban rayuwa.
Ana dai daukar wadannan matakan ne domin hana yaduwar cutar Covid – 19 da ake kira Korona Bairos, fata dai Allah ya tabbatar mana da nasara a koda yaushe.

About andiya

Check Also

The Daily Hug For Appreciation 2023

The daily hug for 28/11/23 is this appreciation of an echo shared by my dear …

Leave a Reply

Your email address will not be published.