….Mun Yaba Da Jinjinar Godiya Ga Gwamnan Jihar Zamfara
Daga Imrana Abdullahi
Alhaji Bashir Nafaru ya yabawa Gwamnan Jihar Zamfara sakamakon irin kokarin da yake na fitar da Jihar daga cikin kangi da halin kakanikayi.
Bashir Nafaru ya ce a madadin ma’aikatan Jihar Zamfara suna mika cikakkiyar godiyar su ga Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal bisa alkairin da yake yi wa ma’aikata, sakamakon hakan muna yi masa addu’ar Allah ya biya masa bukata.
Kuma “muna gayawa al’ummar duniya da cewa za a yi siyasar da ba a taba yin ta ba domin mutum ne za a zaba ba jam’iyya ba don haka ne a yanzu ake ta yin fadakarwa cewa kada ayi jam’iyya a dai yi mutum kawai”.
Ya kara da cewa mu a Jihar zamafara mun ga Gwamnan ya yi abin a ya ba a zo a gani don haka muke cewa Allah ya saka masa da alkairi.
“Hakika a Jihar Zamfara za a yi siyasar da ba a taba yin irin ta ba”, inji Bashir Nafaru.