Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Dalhatu Attahiru Bafarawa, ya bayyana samar da kungiyar fafutukar ganin matasa sun kama ragamar shugabancin Najeriya da cewa wani tsari ne da zai hanyar ceton arewacin kasar da kuma kara karfafa Gwiwar matasa su shiga harkar shugabanci.
Shugabannin arewacin Najeriya kwannan sun kaddamar da kungiyar (The Northern Star Empowerment Initiatives) karkashin jagorancin Bafarawa. Wannan tsarin an yi shi ne da nufin samun hadin kan al’ummar karkara da kuma kara karfafa matasa da nufin shiga harkar shugabanci.
A cikin wata tattaunawa da kafar yada labarai ta BBC hausa, Bafarawa ya bayyana cewa kungiyar an kirkire ta ne domin samun damar warware matsalolin da ke fuskantar arewacin Najeriya,da sula hada da matsalar tsaro, rashin aikin yi, matsalsr Talauci,karancin abinci, da kuma yawan yara wadanda basa zuwa makaranta.
Sai dai Bafarawa ya ce wannan kokarin samar da kungiya ba lamarin siyasa ba ne, kunguya ce mai zaman kanta da ba ta da wata niyyar shiga harkar siyasa ko kuma yin siyasar dungum ta hanyar shiga wata jam’iyya. Kawai ana nemawa yankin Arewa dama ce”, inji Bafarawa.
Bafarawa ya kuma jaddada cewa ba shi da wata niyyar neman wani ofishin siyasa kuma ba shi da nufin shiga gwamnati ko wani mukami na Gwamnatin har tsawon rayuwarsa baki daya, ” Tsakani na da Allah ba ni son a zabe ni, ba ni son duk wani mukamin gwamnati a duk tsawon sauran rayuwarta.Abin da nake so shi ne kawai in tabbatar matasa sun samu damar da ya dace su samu saboda a samu zaman lafiya.
Tsohon Gwamnan ya bayyana damuwarsa a game da irin yadda aka mayar da matasa baya a arewacin Najeriya, ya na mai bayanin cewa an mayar da matasa da dama sun zama shakulatun bangaro duk da irin yadda yankin keda arzikin dimbin matasa. ” Dalilin kafa wannan kungiyar shi ne domin a fadakar, da yi wa matasa jagorancin yadda za su yi shugabanci, domin hakkinsu ne da muke yi wa fafutuka a halin yanzu. Idan Muna son zaman lafiya, lallai sai mun yi wa matasa nuni”, inji shi.
Bafarawa ya bayar da tabbacin cewa dukkan wanda ya shiga wannan kungiya kuma ya na neman wani matsayi na shugabanci lallai kungiyar za ta taimaka masa.ya kara da cewa kungiyar ta samu karbuwa a tsakanin shugabannin Musulmi da Kirista.
Ya bayyana cewa matakin rabuwar Kaduna a tsakanin yan Arewa da aka raba kansu ta fuskar addini, kabilanci, ya karfafa cewa idan har lamarin adfini bai zamo wani abu wani lamarin da rabuwar kawuna ba don haka muke ganin sai an hada kan yan Arewa a kowane bangare, “idan da ba a yi amfani da batutuwan addini ba hakika arewacin Najeriya ba zai rarra ba ba”, inji Bafarawa.. Saboda haka sai Bafarawa ya bayar da shawarar cewa shugabannin addini da su hada kan jama’a a kuma samar da hanyoyin warware matsaloli domin a samar da ci gaba.