Related Articles
Daukar Nauyin Wasanni Halayyar Mu Ce a Kamfanin GAC
Fitaccen kamfanin motoci na GAC ya bayar da tabbacin cewa za su ci gaba da taimakawa harkokin wasanni a Nijeriya, saboda halayyar kamfanin GAC.
Janar manaja mai kula da harkar kasuwanci na kamfanin motocin GAC, Jubril Arogundade ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna ranar Asabar a wajen taron tseren yada kanin wani mai lakabin Marathon, inda kamfaninsa ya kasance cikin masu daukar nauyin Gasar tseren.
Ya bayyana cewa sun dade suna taimakawa harkokin wasanni a kasa baki daya, ya ce wasan tseren yada kanin wani na Jos na kwanan nan da sauran wadanda suka dauki nauyi.
Tun da farko lokacin taron manema labarai da aka yi kafin a fara gasar ranar Juma’a, Mista Arogundade ya ce wannan gasar abu ne mai matukar muhimmanci a wurinsu.
“Gwamnatin Jihar Kaduna ta dauki wanna lamari da matukar muhimmanci lokacin da Nijeriya take neman hadin kai”.
” Muna murnar mu zama a cikin wannan lamarin kuma muna farin cikin daukar nauyin gasar”.
“Muna son kara karfafa Gwiwar dukkan matasa a Jihar Kaduna su kasance suna cikin wannan lamarin, musamman wajen nuna kauna ga Jihar Kaduna”, inji shi.