Home / Big News / An Sace Shugaban APC Na Jihar  Nasarawa

An Sace Shugaban APC Na Jihar  Nasarawa

An Sace Shugaban APC Na Jihar  Nasarawa
 Imrana Abdullahi
Bayanan da soke fitowa daga Jihar Nasarawa na cewa wadansu mutane da suka kutsa kai gidan Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Nasarawa Mista Philip Shekwor sun yi awon gaba da shi.
Kwamishinan Yan Sanda Mista Bola Longe ya tabbatar da faruwar lamarin a lafiya hedikwatar Jihar.
Inda ya tabbatar da cewa mutanen da suka dauke shugaban Jam’iyyar sun je gidan ne misalin karfe 11 na Dare kuma sun tafi da shi wani wurin da ba a san ko’ina bane.
 Mista Bola Longe ya bayyana cewa jami’an tsaro tuni suka dauki mataki da gaggawa inda aka Sanya jami’an tsaron a kowane wuri daban daban domin tabbatar da an kubutar da shugaban Jam’iyyar Philip Shekwor daga hannun wadanda suka sace shi.

About andiya

Check Also

SANATA AMINU WAZIRI TAMBUWAL YA KAWO GAGARUMIN CI GABA A JIHAR SAKKWATO

DAGA IMRANA ABDULLAHI  A kokarin ci gaba da sanar wa duniya irin jajircewar da tsohon …

Leave a Reply

Your email address will not be published.