Home / Labarai / ZA MU CIYAR DA JIHAR KATSINA GABA – DIKKO RADDA

ZA MU CIYAR DA JIHAR KATSINA GABA – DIKKO RADDA

…Za mu tabbatar da tsaron lafiya da dukiyar al’umma
Daga Imrana Abdullahi
Sabon zababben Gwamnan Jihar Katsina Dokta Dikko Umar Radda ya bayyana kudirinsa na tabbatar da aiwatar da ingantattun gyare gyare domin ci gaban Jihar tare da al’ummarta baki daya.
Dokta Dikko Umar Radda ya bayyana wa al’ummar Jihar Katsina cewa an yi zaben da ba a taba yinsa ba a Jihar.
” hakika mun lura jama’a na mantawa ne cewa an yi zaben shugaban kasa tare da wadansu kujerun yan majalisu biyu na tarayya da suka hada da na yan majalisar Dattawa da na Wakilai kuma tazarar da ke tsakanin APC da PDP a yawan kuri’un zaben yan majalisar Dattawan da APC ta lashe duk guda uku tazarar ta kai yawan kuri’u dubu Hamsin
Yawan kuri’u kuma na yan majalisar wakilai guda tara da APC ta samu ya kai dubu sama da Talatin.
“Amma kuri’ar da kake magana ai kuri’a ce kasa da dubu Bakwai kuma lamarin zabe baka rasa shi da nau’in dan kabilancin Bangaranci da na kabilanci amma duk da haka Jihar Katsina ita ce Jiha ta uku da ta ba Tinubu yawan kuri’a a Najeriya, sannan akwai fa bambanci tsakanin zaben Gwamna da na shugaban kasa a bayya ne lamarin yake domin jama’a na can kasa ba su samu da zaben shugaban kasa ba kamar yadda suka samu da zaben Gwamna”.
Agame da batun shari’a kuwa dan gane da zaben Gwamnan Jihar Katsina, Dokta Dikko Umar Radda ya ce a matsayinsu na yan kasa sun san kowa na da damar zuwa kotu ya nemi hakkinsa kuma mu yan kasa ne zamu karbi abin da kotu ta yi hukunci.
“Mu tun kafin zabe mun kai kan mu a kotun Ubangiji cewa duk hukuncin da Allah ya yi a kan mu mun amince da shi, idan mun samu mun godewa Allah idan kuma mun rasa duk mun godewa Allah duk hukuncin da Allah ya yi a kan mu mun Gamsu da shi. Kuma duk wani hukuncin da wani zai yi mun amince da shi kawai dai mun nemi jama’a su zabe mu kuma sun zabi cancanta, kwarewa da kuma wadanda za su rike masu amanarsu da ta dukiya don haka muna yi wa Allah godiya, duk muna godiya ga wadanda suka fito su sama da dubu tari Takwas suka zabe mu kuma muna godiya ga dukkan mutane  Jihar Katsina har ma wadanda ba su zabe mu ba sun zabi jam’iyyun adawa duk mina godiya”, inji Dikko Umar Radda.
Dikko ya kara da cewa kamar yadda ya yi jawabi bayan cin zabensa shi ne ya na kira ga jama’ar da suka yi takara da su zo ayi tafiya tare a hada hannu wuri daya domin kawo wa jama’ar Jihar Katsina ci gaba.
“Na bude kirji da hannaye tare da zuciya ta ina yin kira a gare su da kowa ya zo a hada kai a tabbatar wa da Jihar Katsina ci gaban da ya dace”.
Kuma maganar tabbatar da tsaro ita ce ta farko kamar yadda na yi alkawari a can baya saboda duk abin da muke son aiwatarwa ba zai samu ba sai idan akwai ingantaccen tsaro.
“Ba zan tsaya in rungume hannu kawai sai abin da Soja ko Dan Sanda daga tsakiya suka yi a kan harkar tsaro ba, kuma matsayin ina Gwamna, za mu bayar da ta mu gudunmawar mu samu jama’ar mu a Kauyukan da suke. Kuma Sojoji da yan Sanda za mu ba su kayan aiki muga yadda lamarin zai kasance har a tabbatar da ingantaccen tsaro a Jihar Katsina baki daya.
Game da batun shiga cikin daji kuwa domin samar da tsaro, Sai Dokta Dikko Radda ya ce daman ai a inda ba kasa a nan ake gaddamar ko – kawa, don haka kamar yadda muka fadi ne wato misali duk hanyar da aka ce bata biyuwa domin matsalar tsaro lokacin kamfe duk mun Sanya kafar mu a wurin mun kuma bi ta,Kuma garuruwan da ko jami’an tsaro na tsoron zuwansu duk mu mun je su tare da yin lacca a cikinsu mun yi magana da kamar da ke cikinsu wannan yakamata ace jama’a su amince da mu cewa da gaske muke yi.
Kuma duk inda aka ce ga wata matsala ta samu aka ce ga Gwamna can tare da shugabannin tsaro na binsa a baya, za a kara karfafa wa jama’a Gwiwa amma bance kowane Dajin da za a je da ni za a je shi ba saboda yanayin aikin Gwamna.
“Da an Rantsar da ni zan kafa hukumar da ke kula wa da kanana da matsakaitan Masana’antu a Jihar Katsina da za ta kasance karkashin ofishin Gwamna, domin a Sanya idanu tare da nagartar aiki a tabbatar da abubuwan da za a yi sun je wurin wanda ya dace domin kullum idan muna son yin nasara a kasar mu dole sai mun rika ba mutane abin da ya cancance su da kamata mu ba su domin kaucewa alfarma da don zuciya mu kuma kaucewa wane daga wurin wane ya fito sannan mu samu biyan bukata. Saboda haka ya dace mu Sani cewa mutanen Jihar Katsina da suka Cancanci su samu wani abu sun same shi don haka na ce zan Sanya ta a ofishina zan kula da al’amuranta da duk yadda ake gudanar da ita, domin duk horaswa da bayar da tallafi sai inda ya dace a bayar da shi”.
Dokta Dikko Umar Radda ya ci gaba da yin kira ga daukacin al’ummar Jihar katsina da su kara hakuri domin sai an aiwatar da wadansu Gyare gyare sannan za a samu Canjin da ake bukata don haka ba daga an Rantsar da Gwamnatin Dikko Radda ba ne za a ga Canji, za mu fitar da tsare tsare masu inganci na kawo gyara saboda haka ne muke fatan a ta ya mu da addu’a domin samun nasara idan mun fara zuba wa jama’a ayyukan alkairi”, inji Dikko Radda.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.