Home / News / ZA MU KAFA GWAMNATI TA JAMA’A BAKI DAYA – SANATA UBA SANI

ZA MU KAFA GWAMNATI TA JAMA’A BAKI DAYA – SANATA UBA SANI

….Gwamna Malam Nasiru Ahmad El – Rufa’I Gida Daya Kawai Yake Da Shi A Kaduna
DAGA IMRANA ABDULLAHI
Sanata Uba Sani, dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna ne karkashin jam’iyyar APC ya yi kira ga daukacin al’umma da a cire duk wani bambancin da ke tsakanin Juna domin Ya dace mu hada hannu tare da Juna wuri daya domin yaki da matsalar rashin tsaro saboda lamarin tsaro  harka ce da ta shafi kowa, don haka ba abin da za a yi wasa da shi ba ne.
Sanata Uba Sani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a cibiyar yan jaridu ta kasa reshen Jihar Kaduna.
Sanata Uba Sani da ke wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar Dattawa ya ce “Ya dace dukkan Gwamnonin Najeriya su hadu wuri daya domin tabbatar da cewa kirkirar yana Sandan Jihohi abu ne mai matukar muhimmanci da nufin kowace Jiha ta samu wadatattun yan Sanda da jami’an tsaro”.
” Shi yasa a halin yanzu akwai wani kudiri a gaban majalisar Dattawa da idan ya zama doka yan sintiri za a ba su damar rike bindiga da nufin yin yaki da yan Ta’adda da suke addabar jama’a”, inji Uba Sani.
Saboda “Idan aka yi duba za a ga cewa yawan jama’ar Najeriya ya kai mutane miliyan dari biyu da Talatin,amma yawan jami’an tsaron da suke a Najeriya bai wuce kashi Ashirin ba cikin dari”.
“Idan muka lura za mu iya gane cewa jami’an tsaron yan Sanda,Sojojin kasa, na sama da na ruwa da sauran dukkan jami’an tsaro shin su nawa ne? za mu ga ba su da yawan da ake bukata”.
Sanata Uba sani ya ci gaba da cewa dokokin da ake da su a kan batun harkokin tsaro musamman idan aka samu mutum da makamai (bindigogi) za a ga cewa dokar mai rauni ce saboda kamar yadda dokar take a halin yanzu idan an kama mutum da makamai za a iya yin belinsa, amma a wasu kasashe za a iya daure mutum shekaru Ashirin da biyar 25 kuma a wasu kasashe akwai hukuncin daurin rai da rai, amma a Najetiya idan an kama mutum da makamai kawai dokar mai rauni ce domin za a iya bayar da belinsa, a matsayina na dan majalisar Dattawa a halin yanzu akwai wata dokar da aka kai a majalisa kuma mun yi aiki kwarai domin karfafa dokar batun samun makamai a hannun jama’a, kuma da ikon Allah za a samu nasarar da kowa ke bukata”, inji Sanata Uba Sani.
Kuma abin da mutane ya dace ya gane shi ne” a cikin miyagun makaman da ake da su guda miliyan dari 500 a yankin Afrika nan ta mu , huda miliyan dari Uku duk suna nan cikin Najeriya ne kuma ga dokar mu bata da kwari domin ta bayar da izinin a bayar da mutum beli idan kankama shi da makamai da ya mallaka ba ta hanyar da ta dace ba, wanda a wasu kasashen ba haka bane.
Zan mayar da hankali ne ga yankunan karkara idan an zabe ni Gwamnan Jihar Kaduna, saboda akwai wasu kananan hukumomin da ba ayi masu aikin komai ba suk za mu tabbatar kowa ya samu abin da ya dace a kowace karamar hukumar.
AIKIN GONA
Zamu tabbatar mun karfafa jama’a su hada kai ta hanyar yin kungiyoyin gama kai ta yadda Gwamnati za ta taimake su sosai.
“Kuma a nuna masu hanyar da za su samu taimakon Gwamnati ta fuskar Noma, saboda akwai da yawa da ba su ma san yadda za su samu tallafin Noma na Gwamnati ba duk wannan yana daga cikin kudirin mu da yardar Allah.
KASUWANCI DA MASANA’ANTU
Kamar yadda kowa ya Sani a duk duniya Gwamnan Jihar Kaduna ya yi aiki kwarai har an samu zuba Karin sama da naira biliyan na dala hudu, an samu kamfanin Taki a Chikun, Kamfanin Olam, kamfanin Tumaturi na Jos da sauran wasu kamfanoni da cibiyoyin bunkasa harkokin kasuwanci. Don haka za mu tabbatar mun hada kai da dukkan masu kokarin bunkasa harkokin kasuwa, ta yadda za mu ci gaba daga inda Gwamnatin Malam Nasiru ta tsaya.
ILIMI
Sama da makarantu dubu hudu duk sun lalace amma da irin gyaran da Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin Malam Nasiru ta aiwatar sai da aka samu karin yara yan makaranta da suka shiga makarantun mu a kalla miliyan daya da dubu dari Bakwai, na yaran da suka shiga makaranta kuma a yanzu ba mu da yawan yaran da suka fice ba su zuwa makaranta kamar wasu Jihohi.
“Muna da masaniyar cewa tarihi ba zai mance da abin da Malam Nasiru ya yi ba a fannin bunkasa harkokin ilimi,me ya sa duk masu surutu a kan batun ilimi ina yayansu suke karatu, wssu fa yayansu na kasashen waje suna karatu don haka kada mu siyasantar da harkar ilimi.
Za.mu tabbatar Gwamnatin da zamu yi ta hada kowa da kowa domin ayi aiki tare ko kuma ta hanyar nada wasu ma ko ta yin tarurruka da jama’a.
“Hakika Malam Gwamna Nasiru mutum ne kamar kowa don haka ya yi magana inda ya ce duk inda muka yi kuskure idan Sanata Uba Sani yazo zai gyara ya fadi wannan maganar
“Ina kashe naira miliyan Hamsin a kowace shekara wajen bayar da tallafin karatun marasa karfi a Jihar Kaduna daga cikin arzikin da Allah ya bani.
“Kasancewata na wanda ya san Malam Nasiru da muke tare da shi shekaru Talatin na san shi ko baka son shi ba zaka ce ya kwashi dukiyar jama’a ba, saboda shi mutum ne mai son jama’a kwarai don haka ne yake yi masu aiki tukuru Dare da Rana Safe da Yamma kokarin yin aiki kawai, don haka nan gaba kadan jama’ar Jihar Kaduna za su rika yin irin na mutanen Abuja su rika neman Malam Nasiru domin suna kawar ganinsa”.
“Tabbas za mu yi wa yankunan karkara aiki sosai kamar yadda ake yi a cikin Kaduna da wasu kananan hukumomin da suke zagaye da ita”.
Kuma ni ina yin kira ga daukacin manema labarai a Jihar Kaduna cewa duk wanda yazo ya ce masu ya na yin takara, to, fatko ya fadi abin da ya yi wa jama’a tukuna ba abin da zai yi ba”.
Kuma wani babban lamari shi ne za mu ta fi da mata domin muhimmancinsu saboda rikon Amanar da suke da shi.
” A halin yanzu daga cikin irin arzikin da Allah ya ba ni ina daukar nauyin karatun wadansu jama’a marasa karfi, da a koda yaushe nake kashe makudan kudin da suka kai naira miliyan Hamsin domin taimakawa suma su samu yin karatu kamar kowa, don haka ina ganin shi ne abin da Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i ke cewa Sanata Uba Sani ma na Sanya kudinsa domin aiwatar da wadansu ayyukan inganta rayuwar jama’a”.
Sanata Uba Sani Ya ci gaba da bayanin cewa zan kafa Gwamnatin da za a ta fi da kowa da kowa domin Gwannatin al’umma baki daya za a kafa da yardar Allah.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.