Daga Imrana Abdullahi, Kaduna North west Nigeria
Honarabul Shu’abu Wakili Kafur, ya yi alkawarin yin aiki tukuru tare da tabbatar da cewa shinkafa Honarabul dukkan kayan da ake Nomawa lamarin ya ci gaba da habaka a jihar Katsina.
Shu’aibu Wakili Kafur, mamba ne mai wakiltar karamar hukumar Kafur a majalisar dokokin jihar Katsina kuma tsohon shugaban kungiyar manoma shinkafa ta kasa RIFAN reshen Katsina ya yi wannan alkawarin ne a wata hira da yayi da manema labarai a Kaduna.
A cewarsa, noman shinkafa ya yi habbaka sosai har ya girma sosai a jihar Katsina a cikin shekaru takwas da suka gabata kuma “zamu tabbatar da samun bunkasawa da fadadawa da bunkasa shi domin samun wadatar abinci a Najeriya.
“Za a yi ta ne wajen samar da dokokin da za su tabbatar da ci gaba da samar da kayan amfanin Gona kamar takin zamani, iri da tsiro, maganin kashe kwari, kayan aikin noma da kyaututtuka masu sauki ga manoma da kuma kasuwannin amfanin gonakin da nufin samun amfani mai yawa a Jihar.
Dan majalisar ya ci gaba da cewa, ya kamata manoman jihar Katsina su rika daukar kansu a matsayin masu sa’a domin samun gwamna mai kokari da himma wanda kuma kwararre ne a harkar noma mai kishin inganta kanana da manyan manoma a jihar.
Yanzu da jihar Katsina ke da kamfanonin samar da shinkafa da yawa, bai kamata manoman shinkafa su ji tsoro ba wajen tallata amfanin gonarsu bayan girbi.
Honarabul Wakili Kafur, don haka ya nemi ci gaba da hada kai da gwamnatin jiha da duk masu ruwa da tsaki domin hada hannu wajen bunkasa harkar noma da sauran ayyukan tattalin arziki da zamantakewar gwamnatin Gwamna Dikko Radda da niyyar bunkasa harkokin tattalin arziki a jihar.