Related Articles
Zamu Mamaye Majalisar Wakilai Saboda Dan Majalisa Lawal Rabi’u – Matasa
Imrana Abdullahi
Wadansu gamayyar kungiyoyin matasa daga arewacin tarayyar Nijeriya da kuma wadansu al’ummar Lere sun bayyanawa manema labarai a Kaduna cewa suna yin kira ga dukkan masu ruwa da tsaki game da harkokin shari’ar da ke cikin kotu a kan dan majalisar kasa mai wakiltar Lere da cewa lallai a bari kotu ta yi aikinta hukuncin da ta yanke shi ne kowa zai yi amfani da shi a matsayin madogara.
Kwamared Jabiru Aminu Mai turare daga kungiyar “Northern Youth Parliament” ya shaidawa manema labarai a Kaduna cewa sun yi wa shugaban majalisar wakilai na yanzu duk da cewa dan majalisar da suke yin magana a kansa dan jam’iyyar PDP ne kuma shugaban majalisar wakilai dan APC ne amma duk da haka ya tsaya a kan sai gaskiya ta bayyana hakika muna goyon baya tare da yin jinjina a kan matsayin da ya dauka.
” Ta yaya dan majalisar da ke kan kujera ya daukaka kara a kotu game da shari’ar zaben dan majalisa mai wakiltar Lere a majalisar tarayya, amma za a ce wai sai a mayar da wani a majalisa, ai ya dace ne a bisa doka da tsarin zaman lafiya sai kotun da aka saukakawa kara ta kammala Shari’arta tukunna”.
Yan kungiyoyin sun ci gaba da cewa in dai aka kasa aiwatar da bin doka da ka’ida ba a bari kotu ta kammala aikinta ba to, za su ta fi Abuja su mamaye majalisa domin a tabbatar da adalci a tsarin majalisar Lere da al’ummar Lere baki daya.
“Mu fatarmu a bari a tabbatar da barin yin ka’ida bisa tsarin doka”. Inji su.