Home / Labarai / Zamu Samar Da Wadatattun Kudi Domin Gyaran Tituna A Najeriya – Sanata Babangida Husaini

Zamu Samar Da Wadatattun Kudi Domin Gyaran Tituna A Najeriya – Sanata Babangida Husaini

Daga Bashir Bello, Majalisa Abuja.
Shugaban Kwamitin da ya ke kula da Hukumar da ta ke kula da gyaran Titunan Najeriya  (FERMA,) Sanata Babangida Hussaini, dan Majalisar Datttawa da ke Wakiltar Jigawa ta Arewa maso Yamma ya ce majalisar Dattawa tasha  alwashin ganin titunan Najeriya wadanda suke karkashin Gwamnatin Taraiya kimanin kilomita 38,000 sun sami wadatattun kudin gudanarwa da za su inganta titunan domin jin dadin zirga zirgar yan Najeriya.
Sanata Babangida Husaini Husaini bayyana  haka ga manema labarai a Majalisar Tarayya a Abuja.
Sanatan, wanda Kwamitinsa ya tantance shugabannin gudanarwa na Hukumar ya ce sun gamsu da irin bayanai da mambobobin kwamitin suka gabatar masu na irin kudure kuduren da suka tanada domin  inganta titunan Najeriya.
Saboda haka Sanatan ya ce Majalisar Dattawa za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta samar da wadatattun kudi a kasafin kudi na shekarar 2024 domin ganin an inganta titunan a Najeriya.
Sanata Hussaini ya kara da cewa ingantattun tituna sune kashin bayan kawo ci gaban arzikin kasa da yan kasa saboda haka Kwamitinsa zai saka ido wajen ganin an gina titunan masu inganci don ci gaban Najeriya.
Har ila yau, ya ce kyawawan tituna suna da alaka da yalwatar arziki da samar da tsaro mai inganci domin masu laifi su na amfani da tituna marasa kyau wajen yin fashi da ta’addanci iri – iri a Najeriya. Saboda haka, kwamitin sa ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an aiwatar da tituna masu inganci.
Sanatan ya kuma karyata zargin da ake yi na cewa Hukumar kula da gyaran titunan Najeriya (FERMA) tana gudanar da aiyuka a kan tituna da aka bayar da kwangilarsu. In da ya yi karin haske cewa a kowace kwangila ana ware wasu kudade domin gyara titunan da suka fashe kafin aiki ya zo kansu don matafiya su sami saukin tafiya.
Inda ya bayar da misali da titun Abuja zuwa Kaduna ya ce kwamitinsa ya umarci kamfanin da yake kwangilar sake gina titin da ya cike ramuka a gurare da dama kamar gadar Rijana da wurin juyawa da ke Jere da sauran ramuka saboda akwai kudade da ake warewa domin yin hakan.
Sanata Babangida Hussaini ya roki Yan Najeriya da su rinka ba gwamnati da kamfanoni da aka bawa kwangila hadin kai wajen bin doka da tsare tsare na gudanar da aikin don samun ingantattun tituna da za a dade ana amfana dasu.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.