Home / News / ZAN HADA KAN YAN NAJERIYA – BUKOLA SARKI

ZAN HADA KAN YAN NAJERIYA – BUKOLA SARKI

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP Sanata Dokta Abubakar Bukola Sarki ya tabbatarwa masu zaben tantakarar shugaban kasa (deliget) a Jihar Kaduna cewa in sun bashi damar ya zama dan takarar har nasara ta samu ya zama shugaban Najeriya zai hada kan daukacin yan Najeriya domin a samu ci gaban da kowa ke bukata.kuma ba zan ci amanar kowa ba.
Tsohon shugaban majalisar Dattawa ta kasa Abubakar Bukola Saraki ya bayyanawa masu zaben dan takarar tare da sauran jama’a a Kaduna lokacin da ya je domin ya gana da su kuma ya bayyana masu kudirinsa ga daukacin Kasar idan ya zama shugaban kasa.
Saraki ya ce sai da hadin kai sannan za a samu ci gaban ilimi,lafiya,Aikin Noma da kasuwanci da dukkan bangarori na rayuwa baki daya.
“Ni da kuke gani na nan zan yi maku aiki domin kasa ta ci gaba na San matsalolin da kasa ke fuskanta kuma ina da kyawawan tsare tsaren warware su baki daya”.
Sanata Abubakar Bukola Saraki kenan lokacin da yake a gaban deliget a Kaduna
Ya fadakar da jama’ar Jihar Kaduna cewa a lokacin da “ina aikin Banki na san Kaduna sosai domin muna zuwa neman masu hulda da Bankin don haka na san Kaduna akwai wuraren hada hadar kudi sosai don haka zan dawo da masana’antu kamar irinsu masaku da dimbin kamfanoni daban daban da suke a Jihar Kaduna, kuma ina yi maku alkawarin cewa zan yi maganin matsalar tsaron da ke addabar arewacin Najeriya domin sai da kwanciyar hankali da zaman lafiya ake samun ci gaban da kowa ke bukata”.
Saraki ya kuma tabbatarwa da masu zaben dan takarar shugaban kasa cewa zai yi amfani da kwarewarsa ta zama Likita, mai’kacin Banki, tsohon Gwamna Shekaru Takwas da kuma Sanata shugaban majalisar ma baki daya ya kawo wa Najeriya da yan kasa gagarumin ci gaban da kowa zai yi farin cikin kasancewarsa dan Najeriya.
Daga cikin wadanda suka tofa albarkacin bakinsu a wajen wannan taro akwai Sanata kuma tsohon minista Ibrahim Musa Kazaure, wanda ya shaidawa jama’a cewa in dai yan Najeriya suna son ganin abin da ya dace na ingantar rayuwarsu to, su ba Sanata Abubakar Bukola Saraki amanar kuri’unsu domin mutum ne da kotun kolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin cewa shi bai yi sata ba saboda haka amintacce ne.
Da yake magana da manema labarai Sanatan yankin Kudancin Kaduna Sanata Danjuma T. La’ah cewa ya yi sun yi aiki tare da Bukola Saraki ya san shi sarai Iran ya ce zai yi kaza to hakan yake nufi lallai zai aikata, don haka mutum ne da za a bashi Amana.
Daga cikin wadanda suka gabatar da jawabai a wurin taron domin yin kira ga masu zaben dan takarar shugaban kasa sun hada da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna mai girma Dallatun Zazzau Alhaji Dokta Ramalan Yero da shugaban PDP na Jihar Kaduna Mosta Felix Hassan Hyat da dukkan shugabannin jam’iyyar na Jihar Kaduna da kuma dimbin yan tawagar Bukola Saraki an dai yi taro lafiya an kuma kare lafiya.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.