Home / Labarai / ZAN SAMAR DA GIDAN TALBIJIN A MAZABAR FUNTUWA – ASAS

ZAN SAMAR DA GIDAN TALBIJIN A MAZABAR FUNTUWA – ASAS

Zamu Yi Aiki Da Malamai,Hakimai, Dagatai Da Masu Inguwanni

Daga Imrana Abdullahi

Dan takarar kujerar majalisar dokoki ta tarayya domin wakiltar kananan hukumomin Funtuwa da Dandume daga Jihar Katsina matashi Alhaji  Abubakar Muhammad Asas.

Abubakar Muhammad Asas, ya bayyana cewa tuni an samu Lasisin gina gidan Talbijin domin kara inganta harkokin fadakarwa, Nishadantarwa da kuma Fadakarwa kamar yadda yake a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Abubakar Asas, ya ci gaba da bayanin cewa shi a matsayinsa na dan takarar kujerar majalisar wakilai da ya kasance matashi domin ya wakilci mutanen karamar hukumar Funtuwa da Dandume a majalisar wakilai ta kasa ba shi da wani Burin da ya wuce kara inganta rayuwar mutanen wannan mazaba da ke kananan hukumomin Funtuwa da Dandume.

“Ni ina fadin cewa kuma har a cikin zuciya ta hakan lamarin yake ba ni da wani biri da ya wuce bayar da gudunmawata wajen taimakon mutanen da suka kasance suna da karamin karfi a cikin al’umma, domin ni ina da abin yi da nake samun abin duniya da har nake taimakawa jama’a da dama da shi kuma ina yi wa Allah godiya da wannan ni’imar da ya yi Mani, shi yasa nake cewa in dai ina neman wannan kujerar ne domin kada in taimakawa al’umma to, Allah ya canza Mani da wani abu da ya fi wannan kujerar, saboda ina nema ne ba domin kaina ba”, inji Asas.

” ina son mutanen kananan hukumomin Funtuwa da Dandume su Sani cewa ni zan ci gaba da nemowa jama’a ne abubuwan da zai inganta rayuwarsu a cikin duniya, domin Allah ya yi mana ni’ima da sanin jama’a a cikin duniya kuma ina da tabbacin za su taimakawa mutanen da zan wakilta, Sabida haka ba sai an samu kudin Kasafin kudi ba zan yi wa jama’a aikin da rayuwarsu za ta inganta ba, zuwa zan yi in mema daga wurin al’ummar duniya kuma za a dace”.

Saboda haka nake ganin cewa ya dace mutanen kananan hukumomin Funtuwa da Dandume su tabbatar sun kada kuri’unsu ga jam’iyyar PDP domin samun nasara ta riba ce a gare su, ba sai na fadi ba kowa ya Sani cewa ko’a haka ina bakin kokari na wajen inganta harkokin al’umma kamar yadda Allah ke taimakona a koda yaushe.

A game da batun matsalar tsaron da ake fama da shi kuwa a wannan matsalar? Abubakar Asas,ya ce zai mayar da hankali wajen yin addu’o’i domin neman taimakon Allah madaukakin sarki ya warware matsalar

” Zan tara dukkan malaman addini a kowace irin kungiya Malami yake domin ayi addu’ar samu warakar matsalar tsaron da ake fama da ita domin haka lamarin ke bukata ayi ta addu’a, zan kuma yi tafiya tare da masu Unguwanni,Dagatai da Hakimai duk baki daya kowa za a bashi hakkinsa da martabar da Allah ya bashi a koda yaushe ba tare da gajiyawa ba,fayan mu a samu nasarar inganta al’amuran rayuwar jama’a kowa a cikin birni da karkara ya samu gudanar da harkokinsa a cikin kwanciyar hankali da lumana”, Inji Asas

“Kuma za mu ci gaba da ayyukan taimakon marayu,Nakasassu da daukacin gajiyayyu baki daya domin neman falalar Ubangiji, saboda haka nake yin kira ga al’umma mazabar kananan hukumomin Funtuwa da Dandume da du ba ni dama ta in wakilce su a majalisar wakilai ta tarayya za su samu ci gaban da ba su ta ba samu a can baya ba, wannan tabbaci ne nake ba su”, inji Abubakar Muhammad Asas

About andiya

Check Also

Sokoto APC supporters take over major streets for Aliyu Sokoto’s victory

  By Suleiman Adamu, Sokoto   It has been jubilation all through by thousands of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.