Home / Labarai / ZAN YI WA KOWA ADALCI A JIHAR KADUNA – JONATHAN ASAKE

ZAN YI WA KOWA ADALCI A JIHAR KADUNA – JONATHAN ASAKE

….Dan takarar Gwamna Na Jam’iyyar Lebo, Asake, Ya Gana Da Malaman Addinin Musulunci, Ya Ba Su Tabbacin Yin Adalci Ga Kowa
Daga Imrana Abdullahi
Honarabul Jonathan Asake, dan takarar Gwamna na Jam’iyyar Lebo a  Jihar Kaduna,ya ba al’ummar Musulmi tabbacin cewa Gwamnatin da zai jagoranta za ta yi aiki bisa gaskiya da adalci da kuma tafiya da kowa, kamar yadda lamarin yake a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun James Sani Swam, mai taimakawa dan takarar Gwamnan jam’iyyar Lebo a Jihar Kaduna Jonathan Asake, da aka rabawa manema labarai.
Asake ya bayar da tabbacin ne a Zariya a lokacin da shi kansa da dan takarar mataimakin Gwamnan Jihar karkashin jam’iyyar Lebo,Honarabul Bashir Aliyu Idris suka hadu da malaman addinin musulunci na Musulmi a kokarin da suke yi na tattaunawa da masu ruwa da tsaki a cikin Jihar.
Kasancewar shugabannin addinin musulunci da suke tare da dimbin jama’a, wadanda mafi yawa daga cikinsu matsalar rashin yin ingantattun shirye shiryen Gwannati APC ya shafe su, don haka ya na da matukar muhimmanci mu nemi addu’arku, da taimakonku domin tattauna wa ta yadda za a samu hanyoyin ci gaba a Cikin Jihar.
Dan takarar Gwamnan ya ce zai tabbatar da kare hakkin duk wani mutum su aiwatar da suk wata damar da tsarin mulki ya ba su domin yin addininsu a koda yaushe, ya kara da cewa yin aiki tare da kowa ne abin da zai aiwatar.
Takardar da aka rabawa manema labaran na cewa, Asake, na shawartar malaman addinin zai yi aiki tukuru wajen magance matsalar tattalin arziki da kuma taron lafiya da dukiyar jama’a, a Jihar don haka ya dace malaman su jawo hankalin jama’a game da irin abin da ya dace su zaba a ranar 11 ga watan Maris.
“Na gabatar da kai na ne gare ku, domin neman addu’oinku da taimakonku domin a samu bukata ta biya nufi, in zama Gwamnan Jihar Kaduna a ranar 11 ga watan Maris da nufin muyi aiki tare wajen ciyar da Jihar gaba ta yadda jama’a za su samu karfin Gwiwa.
“Zan tabbatar da yin gaskiya da adalci ga kowa a Jihar Kaduna, San yi amfani da aiki da tsarin gaskiya kamar yadda yake a cikin kundin tsarin mulkin kasa na shekarar 1999. Zai kare kowa da inganta lamuran kowa da kowa domin kowa zai yi aiki da damar da yake da ita kamar yadda kundin tsarin mulki ya bashi dam”, kamar yadda yake a kunshe a cikin takardar da aka rabawa manema labara.
Ya bayyana cewa Talauci,rashin aikin yi,Satar jama’a, kisan jama’a ba gaira ba dalili da matsalar bambancin addini da kabila duk sun samu ne sakamakon matsalar rashin ingantaccen shugabanci a Jihar don haka ne Asake ya ce zai tabbatar da yin gyara ba tare da ba ta lokaci ba a matsayinsa na jagora a Jihar.
Ya ci gaba da cewa idan shugabanni ba za su yi aiki da tsarin yin tafiya da kowa ba tare da tausayawa jama’a, sai zamanto ana ta samun matsaloli a kowa ne fanni.
Asake ya gayawa malaman addinin cewa jam’iyyar Lebo ce kawai da ke da tsarin kyautatawa al’umma a matsayin abin da za ta aiwatar a kullum wanda hakan ya sa suka Sanya shi a matsayin alamar su ta jam’iyyar da ya nuna Uba,Uwa da yaya a matsayin alamar jam’iyyar. Ya ce a matsayin jam’iyyar ma’aikata da al’umma na can kasa, hakika mutanen Jihar ba za su yi da na Sani ba idan sun zabi jam’iyyar Lebo, (Labour Party).
Malamin addinin wanda ya yi magana a madadin sauran malaman, Imam Shugaba Abdulhamid Muhammad,ya shawarci dan takarar Gwamnan da ya tabbatar da cika alkawari idan ya samu nasarar zama Gwamnan Jihar Kaduna, ya kara da cewa hakika ya na da matukar amfani ya bude kofarsa ga kowa”domin kowa da suka hada da Talakawa su samu damar yin magana da hulda da Gwamnati.
Sai Malamin ya bayyana bacin ransa da irin yadda wadansu mutane idan an zabe su sai su shiga madafun iko su kulle kofarsu ga kowa,”don haka mu idan mun ga abin da aka yi ba dai- dai ba w wajen tafiyar da mulki, hakika za mu bayyana rashin jin dadin mu a fili”.

About andiya

Check Also

Sokoto APC supporters take over major streets for Aliyu Sokoto’s victory

  By Suleiman Adamu, Sokoto   It has been jubilation all through by thousands of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.