Home / Labarai / Zulum Ya Ziyarci Dikwa Ya Rabar Da Miliyan 115, Kayan Abinci Ga Mutane Dubu 34

Zulum Ya Ziyarci Dikwa Ya Rabar Da Miliyan 115, Kayan Abinci Ga Mutane Dubu 34

Zulum Ya Ziyarci Dikwa Ya Rabawa Miliyan 115, Da Bayar Da Kayan Abinci Ga Mutane Dubu 34
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Borno Furofesa Babagana Umara Zulum ya ziyarci garin Dikwa wajen duba aikin rabon kayan abinci ga mutane dubu 34 domin taimakawa ga marasa galihu mata da mazaje masu jagorantar gidajensu daban daban.
Gwamna Zulum ya kuma yi alkawarin samar wa wadansu mutane masu aikin sa kai lafiya a karkashin tsarin musamman a ko ina cikin fadin duniya.
Mata dubu 23 sun samu kudi naira dubu biyar, daga cikin naira miliyan 115, sai Maza dubu 11da suke shugabantar iyalansu da aka ba su Buhunan Shinkafa da Wake, Buhun garin Masara da kuma fakitin Man Girki.
 Wannan rabon kayan abinci an yi shi ne domin taimakawa mutanen da suka samu matsalar lalacewar sana’o’i da kuma rasa hanyoyin neman abincinsu sakamakon ayyukan Boko Haram, wanda hakan ya hana su samun kudi da kayan abinci, hakan ta Sanya suke samun saukin mayar da su cikin kungiyar Ta’adda daga cikinsu bayan sun Kassara su.
Bayan wannan rabon kayan jin kai ga mutanen Dikwa, sai Gwamnan ya ziyarci babban asibitin Gwamnati da kuma karamin asibitin shan magani duk a cikin garin Dikwa.
Gwamna Babagana Umara Zulum ya kuma bayar da umarnin samawa wadansu masu aikin sa kai guda 9 asibitin musamman domin nema masu magani a ko’ina , sun dai samu matsala ne lokacin da yan Boko Haram suka kai masu hari a Dikwa, kuma nema masu maganin ya hada har ma idan za a kaisu kasashen waje ne duk a shirye muke domin yin hakan.
Yan aikin Sa kan suna daga cikin dubban mutanen da suke taimakawa jami’an tsaro na sojoji a wajen yaki da yan Boko Haram sun dai samu raunuka ne daban daban wasu ma har sun rasa kafafunsu sanadiyyar hakan suka zama Giragu.
Kafin batun neman lafiyar Gwamna Zulum, ya amince da kudin alawus da kashi dari bisa dari ga wasu masu aikin sa kai guda Tara (9).
Zulum ya kuma yi ta’aziyya ga dukkan daukacin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon irin kokarin da suka yi na aikin sa kai a shirin hadin Gwiwar jami’an tsaro da nufin kawo karshen yan Boko Haram a wasu yankunan Jihar Borno.

About andiya

Check Also

Senator Yar’adua Donates Books To Schools In 11 LGAs

By Lawal Gwanda Senator Abdul’aziz Musa Yar’adua of Katsina Central Senatorial District has donated assorted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.