Home / News / Zuwa ga Alh Ahmed Ibrahim Lawan Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya

Zuwa ga Alh Ahmed Ibrahim Lawan Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya

Zuwa ga Alh Ahmed Ibrahim Lawan
Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriy
Zargin kai wa shugaban hukumar  kula da tashoshin jiragen ruwa, Hadiza Bala Usman da aka kai wa hari a majalisar kasa.
A matsayin mu na kungiya mai cikakkiyar rajista a Nijeriya da ke fafutukar ganin an samu ingantaccen canji mai amfani da Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta Kawo karkashin jam’iyyar APC hakika muna tare da wannan tsarin domin ci gaban kasa da al’ummarta baki daya.
Haka kawai, ba za mu damu da rubuta maka wannan wasikar ba, saboda mun san kai da sauran jagororin majalisar dattawa ta kasa na ta kokarin lalubo hanyoyin warware matsalolin da suke fuskantar kasa.
Don haka, muna rokon ka arziki kawai ka ta fi kai tsaye domin yin abin da ya kamata.
Mai girma shugaban majalisa, idan za ka iya tuna wa manajar darakta ta hukumar kula da tashoshin jiragen ruwan Nijeriya, Hadiza Bala Usman ta zo majalisar dattawa a ranar 3 ga watan Disamba 2019 domin ta amsa gayyatar da ‘yan majalisa suka yi mata a kan batun bincike da sauraren
Mai girma shugaban majalisa, idan za ka iya tunawa shugabar hukumar kula da tashoshin zirga-zirgar jiragen ruwa ta kasa, Hadiza Bala Usman ta zo majalisar Dattawa a ranar 4 ga watan Disamba 2019
bisa gayyatar da aka yi mata domin ganin ta girmama majalisar a kan batun ayyukan kamfanin OMSL da wasu hukumomin tsaro a birnin Legas.
Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa kwanan nan ne ta shaida wa rundunar sojojin ruwa a game da matakin da ta dauka dakile wata barakar da ke haifar da zurarewar kudi da suka kai a kalla Biliyan Hamsin (50) da wani kamfani mai zaman kansa yake caza, mai suna OMS.
A matsayinta na mai ganin girman majalisar dattawa, ba ta taba kin amsa gayyatar da aka yi mata ba. Ta amsa kiran kuma ta yi bayani a fili cewa “hukumar kula da tashoshin jiragen ruwan ba ta da bukatar wani kamfani mai zaman kansa ya yi wannan aikin, saboda Gwamnatin Nijeriya ta hannun NN, NIMASA da kuma hukumar kula da tashoshin ruwan za su kula da tsaron hanyoyin ruwan ba tare da masu jiragen sun biya ko sisin kwabo ba. Saboda a halin yanzu ana kokarin ganin an tattala dan abin da ke nan a Nijeriya don haka irin wancan kashe kudin da muka soke na daga cikin abin da ke zaman wani karin kashe kudi a tashoshinmu.
Saboda haka bisa irin kokarin da hukumar tabbatar da tsaron hanyoyin ruwan Nijeriya NIMASA ke yi da gwamnati ke kashe biliyoyin Dalar Amurka, me kuma za a yi da wani abu na daban kuma ana son tattalin dan abin da ke hannun gwamnati
Bayan ta kammala tattaunawa da ‘yan majalisar lokacin da take kokarin fita daga wurin sai kawai wadansu da ake zargin biyansu aka yi domin sai kawai suka dinga hargowa suna kokarin fada nata.
Mene ne laifinta a nan? An kira ta ne domin yin bayanai a kan wani kamfani OMSL. Kamar yadda ta bayyana cewa lokacin da wani mai suna Dakta Idahosa Wells Okunbo ya kammala bayaninsa an gan shi rai a bace yan kokarin sai shugaban kwamitin hadin gwiwar ya dakatar da zaman. A lokacin ne ake zargin cewa yaran Okunbo suka yi ta yi mata hargowa da kalamai kala-kala suna son a fili sai sun kai mata hari.
Saboda haka mu ba za mu amince da irin wannan lamarin ba musamman da suka aikata wannan aikin rashin biyayya kuma lamarin ya faru ne a majalisar dattawa, a halin da ake ciki a yanzu mutane za su dauka cewa da zarar majalisar ta gayyaci wani babban jami’in Gwamnati mace ne ko namiji hakika za a tabbatar wa da mutum cikakken tsaro da ya cancanci ya samu, amma sai gashi lamarin ya zama sabanin hakan.
Muna son cewa daukacin ‘yan Nijeriya da kuma majalisar dattawa su sani ita wannan baiwar Allah tana yin aikinta ne domin ci gaba da tabbatar wa tashoshin ruwan Nijeriya martabar da suke da su tun asali, don haka ba za ta saurara wa duk wani da aniyarsa ta saba da hakan ba domin ba za a bari yana ba ta su ci galaba kan Nijeriya ba kuma za ta ci gaba da gudanar da aikin kishin kasa ko da za ta rasa ranta ne.
Kamar yadda wasu suka dauka cewa su ne ke da Nijeriya sun mance cewa ita wannan baiwar Allah diya ce ga wani babban malamin jami’ar Ahmadu Bello wanda duk a ciki da wajen Nijeriya aka san da shi kuma aka amince da shi baki daya.
Sakamakon irin aikin da take yi tukuru domin ci gaban kasa ya sa wadansu kamfanonin yada labarai na duniya suka ba ta lambar yabo tare da karramawa daga cikinsu akwai jarida mai magana a kan kudi da tattalin arziki (Financial Times) da suka ba ta lambar karramawa a matsayin mace mai kamar maza a shekarar 2014, hakazalika kafar Talbijin ta CNN sun ba ta lambar karramawa a shekarar 2014, sai Mujallar Ebony a matsayin mace a cikin fitattun mata dari da suka kasance bakar fata a cikin duniya su ma a shekarar 2014 kuma mamba a cikin mata masu aji a shekarar 2018 a tsakanin mutanen kasashen Afirka ( MIPAD) tsari ne da asusun majalisar dinkin duniya ke ba tallafi mai lamba 68/237 na shekaru aruaru na mutanen Afirka.
A watan 30 ga watan  Nuwamba 2017, ta karbi lambar karramawa ta kamfanin Jaridar harkokin kasuwanci (Business day) da ke kan gaba wajen yada al’amuran kasuwanci a tarayyar Nijeriya
Sai kuma kamfanin yada labarai na  DAAR da suka ba ta lambar karramawa ta gudanar da kyakkyawan shugabanci a harkar mulki da ya shafi ayyukan da ake gudanarwa a bangaren gwamnati, saboda kokarin da ta yi na tsafta cewa tare da kara inganta harkokin aiki a hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa.
Kuma ita ce mataimakiyar shugabar yankin Afirka na gamayyar kungiyar kasa da kasa masu tashoshin jiragen ruwa ( IAPH)
Ta zo ne domin yi wa Nijeriya aiki kuma a shirye take domin aiwatar da aikin. Saboda haka idan wani baya son yin biyayya ga dokar aikin gwamnati kowa ne ba zai samu biyan bukata ba a kodayaushe. A matsayin ta na yar asalin Jihar Katsina, muna alfahari da ita tare da ayyukan da take gudanarwa saboda haka duk wani mai aiki sabanin haka ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen sa kafar wando daya da shi musamman ga duk mai son kawo wa kokarin da take yi cikas.
Sakamakon haka ne ya mai girma shugaban majalisar dattawa muke kira gare ka da ka kafa kwamitin bincike domin bincika wadanda ke da hannu a cikin wannan lamari in har majalisa na son jama’a su ci gaba da yi masu kallon martaba.
In har wannan lamari ya ta fi haka kawai ba tare da an hukuma wadanda suka aikata hakan ba, zai sa yan Nijeriya su canza tunani a kan majalisar musamman idan aka gayyace su zuwa majalisar
Majalisar dattawa karo ta tara da ta kasance a karkashin jagorancin ka na da nauyin gudanar da bincike tare da yi wa duk wani mutum ko mutane hukunci idan an same su da hannu a abin da ya faru domin ya zama darasi ga masu son yin hakan a nan gaba.
Darakta Janar,
Alh Sallau Arawa
Na kungiyar matasan Katsina masu fafutukar ingantaccen canji
(Katsina Youth for Sustainable Change)

About andiya

Check Also

Edo 2024: Group Hold Symposium In Support Of Asue Ighodalo

  The Good Governance Advocacy Group, has held a symposium to drum their support for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.