Home / Labarai / Allah Ya Yi Wa Kanar Aminu Isa Kontagora Rasuwa

Allah Ya Yi Wa Kanar Aminu Isa Kontagora Rasuwa

Allah Ya Yi Wa Kanar Aminu Isa Kontagora Rasuwa
Mustapha Imrana Abdullahi
Sakataren Gwamnatin Jihar Neja Ahmed Ibrahim Matane ya bayyana kaduwarsa da jin rasuwar tsohon Gwamnan Jihohin Kano da Benuwai kanar Aminu Isa Kontagora, ritaya.
Kanar Aminu Isa Kontagora ya rasu ne a Abuja bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
A cikin sakon ta’aziyyarsa sakataren Gwamnatin Jihar Neja ya bayyana rasuwar Aminu Isa Kontagora a matsayin wani al’amari na kaduwa inda ya ce hakika marigayin mutumin kirki ne mai hakuri da kamala da za a rika tuna shi da ya yi kokari kwarai wajen bunkasa Jihohin Kano da Banuwai lokacin da ya zama Gwamnan mulkin soja a Jihohin.
Kamar yadda Ahmed Matane ya bayyana “marigayi kanar Aminu Isa Kontagora mutum ne da ake girmamawa da ya sadaukar da rayuwarsa wajen kokarin ciyar da Jiha, Kasa da kuma inganta daraja da rayuwar jama’a baki daya gaba, hakika rasuwarsa wani babban rashi ne da ya bar gibi mai wuyar cikewa”.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun jami’in yada labarai a ofishin sakataren Gwamnatin Jihar Neja Lawal Tanko.
“A madadin Gwamnatin Iihar Neja da daukacin al’ummar Jihar baki daya muna mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayi Aminu Isa Kontagora, Sarkin Sudan, Kontagora, Alhaji Sa’idu Namaska, mutanen masarautar Kontagora bisa wannan babban rashin”, inji sakataren Gwamnatin Jihar Neja.
 Ya kuma yi addu’ar Allah madaukakin Sarki da ya jikan marigayin ya kuma bashi Aljannah Firdausi ya kuma ba iyalan hakurin jure wannan rashin.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.